Labarai
Gwamnatin Jigawa ta Amince da Shirin Ci gaban Al’umma na Kudin Akwati
Daga Usman Muhammad Zaria
Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da rahoton Kwamitin Asusun Ci gaban Akwatin Zaɓe (Kudin Akwati)
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Dakta Nura Ibrahim ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar.
A cewarsa, Majalisar Zartarwar ta amince da rahoton kwamitin da aka kafa kan shirin kudin akwati, tare da miƙa rahoton zuwa ga Majalisar Dokokin jihar domin su ɗauki matakin kafa doka kan gyaran babbar Dokar Ci gaban Al’umma ta Jihar Jigawa ta shekarar 2018.
Ya ce wannan shiri ya yi daidai da manufofin gwamnatin Namadi, musamman wajen bunƙasa ci gaba, kyautata jin daɗin jama’a, da tabbatar da cewa kowa ya samu damar shiga harkokin ci gaba.
Dakta Kazaure ya ƙara da cewa, wannan muhimmin shiri zai bai wa mutane da al’ummomin karkara damar samun tallafin kuɗi domin aiwatar da muhimman ayyukan gyara ko kula da kayayyakin more rayuwar jama’a, kamar gyaran rijiyoyin burtsatse, magudanan ruwa, kujeru da tebura na makarantu, da sauran makamantansu.
Ya kuma ƙara da cewa, shirin zai zama wata hanya ta gwamnatin jihar wajen isar da amfanin dimokuraɗiyya ga dukkan al’ummar jihar, ta hanyar hanzarta ayyukan ci gaban al’umma a matakin ƙasa, kawo gwamnati kusa da jama’a, tare da rage tsaiko da jinkirin da ake samu a harkokin gudanarwa.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
