Labaran Gida
Kungiyoyin Agaji da WFP Sun Ƙaddamar da Cibiyar Busar da Amfanin Gona ta Hasken Rana Mai Darajar ₦100m
Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP), tare da haɗin gwiwar Gidauniyar Mastercard, kuma Self Help Africa ke aiwatarwa, sun ƙaddamar da cibiyar busar da amfanin gona ta hasken rana mai darajar naira miliyan 100 a Ƙaramar Hukumar Kura ta Jihar Kano, domin samar da hanyoyin dogaro da kai masu ɗorewa ga matasa 5,000 a banagren aikin gona.
Wannan shiri na daga cikin ƙoƙarin faɗaɗa tsarin samar da abinci da kuma bunƙasa ci gaban kasuwanci a faɗin jihar.
Da take jawabi a wajen ƙaddamarwar, Daraktar Self Help Africa a Nijeriya, Joy Aderele, ta bayyana cibiyar a matsayin sauyi daga tsarin tallafin agaji na gargajiya zuwa samar da ayyukan yi da bunƙasa kasuwanci.
Ta ce cibiyar za ta samar da ayyukan yi kai tsaye ga matasa a Kura da yankunan da ke kewaye, musamman a fannin noman kayan lambu da ƙara darajar amfanin gona.
Aderele ta lura cewa Kura ta shahara wajen noman kayan lambu, musamman tumatir, barkono da albasa, waɗanda ake kaiwa kasuwanni a Kano da ma sauran wurare.
Sai dai ta bayyana cewa manoma kan fuskanci asara mai yawa a lokacin yawaitar amfanin gona sakamakon ƙarancin wuraren ajiya da faɗuwar farashi a kasuwa.
Ta ce, “Idan amfanin gona ya yi yawa kuma babu isasshen ajiya, manoma kan yi asarar kuɗaɗensu, kuma amfanin gona ya lalace,” tana mai ƙara da cewa cibiyar busar da hasken rana na ba da mafita mai amfani ga wannan matsala.
A cewarta, fasahar da ke amfani da hasken rana na bai wa manoma da matasan ’yan kasuwa damar adana amfanin gona, ƙara masa daraja da tsawaita lokacin ajiyarsa, ta yadda za su iya sayarwa bayan lokacin girbi.
A nata jawabin, wakiliyar WFP, Esther Ogundari, ta yaba wa hukumomin ƙananan hukumomi da shugabannin al’umma bisa goyon bayan da suka bai wa shirin, tare da ƙarfafa matasa, musamman mata, da su amfana da damar domin ƙara samun kuɗaɗen shiga.
Ta jaddada gagarumar damar noma da Kura ke da ita, inda ta ce samuwar ruwa da ƙasa mai kyau na ba yankin damar ƙara yawan amfanin gona da faɗaɗa kasuwanni.
Da yake ƙaddamar da cibiyar, Shugaban Ƙaramar Hukumar Kura, Alhaji Rabiu Abubakar, ya bayyana ta a matsayin irinta ta farko a yankin, yana mai cewa za ta taimaka ƙwarai wajen haɓaka aikin noma zuwa matsayi na duniya.
Hakimin Gundumar Kura, Alhaji Lamido Abubakar, ya yi kira da a kula da cibiyar yadda ya dace tare da tabbatar da ɗorewarta, domin ta cimma manufofin da aka kafa ta.
Da yake magana a madadin waɗanda suka amfana, wani mai larurar nakasa, Malam Rabi’u Balarabe, ya ce an horas da shi kan dabarun zamani na busar da kayan lambu da sauran amfanin gona masu saurin lalacewa, da kuma tsara kasuwanci domin amfani da cibiyar yadda ya kamata.
Ya bayyana fatan cewa cibiyar za ta ƙara kuɗaɗen shiga tare da rage asarar amfanin gona ga ƙananan manoma.
Dangane da ƙarfin fasahar cibiyar, jami’an aikin sun ce cibiyar ta ƙunshi na’urar busar da hasken rana da ke iya busar da tan ɗaya na tumatir cikin sa’o’i huɗu zuwa shida, da kuma na’urar busar da UV wadda ke kare amfanin gona daga lahani yayin sarrafawa.
Ana sa ran wannan ƙirƙira za ta rage asarar amfanin gona bayan girbi da kusan kashi 50, lamarin da zai ƙara kuɗaɗen shigar manoma tare da inganta kare muhalli.
Cibiyar na aiki ne a matsayin kasuwancin al’umma da ƙungiyoyin haɗin gwiwa ke gudanarwa domin tabbatar da ɗorewa, inda manoma ke biyan kuɗi kaɗan bisa ayyukan da aka yi musu.
Khadijah Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
