Labarai
Shugaba Tinubu Zai Halarci Bikin Kamun Kifi da Al’adu na Argungu
Daga Sani Haruna Dutsinma
Gwamnatin Jihar Kebbi ta bukaci mazauna jihar da yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kyakkyawar tarba tare da nuna farin ciki yayin ziyararsa zuwa jihar a ranar Asabar, 14 ga watan Fabrairun 2026.
Malam Yahaya Sarki, Mashawarci na Musamman ga Gwamnan Jihar Kebbi kan Harkokin Yada Labarai ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.
Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu zai kai ziyara jihar domin bude wasu manyan ayyuka da gwamnatin Gwamna Nasir Idris ta aiwatar, tare da halartar bikin al’adu da kamun kifi na Argungu karo na 61 wanda ya fara a yau Laraba 11 ga watan Fabrairun 2026.
Kwamishinan Harkokin Labarai da Al’adu, Alhaji Yakubu Ahmed, ya roki hadin kan al’ummar jihar, yana mai jan hankalin su da su bayyana kyakkyawan dabi’un su ga manyan baki daga ƙasashen duniya.
Sanarwar ta bayyana cewa ayyukan da Shugaban ƙasa zai bude sun haɗa da Sakatariyar Gwamnati da aka sawa suna Bola Ahmed Tinubu, da babbar tashar motar Birnin Kebbi, da sababbin hanyoyi a cikin birni, da tagwayen hanyoyi na Argungu, da sauransu, kafin ya halarci bukukuwan al’adun.
Haka kuma, za a rufe wasu hanyoyi a cikin Birnin Kebbi da wasu sassan Argungu na ɗan lokaci domin sauƙaƙa zirga-zirgar shugaban ƙasa bisa ƙa’idojin tsaro, sannan an bukaci al’umma da su kasance masu bin doka, zaman lafiya, da nuna kyawawan ɗabi’u.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
