Ilimi
Gwamnatin Jigawa ta Sami Gagarumin Cigaba a Bangaren Ilimi- Gwamna Namadi
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce jarin da take ci gaba da zubawa a bangaren ilimi ya fara haifar da sakamako mai kyau, musamman a matakin ilimin firamare a fadin jihar.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan yayin da ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki a bangaren ilimin firamare, wanda aka shirya domin duba irin ci gaban da aka samu, kalubalen da ake fuskanta da kuma damar da ke akwai.
An gudanar da taron ne a Fadar Gwamnati da ke Dutse.
Gwamna Namadi ya nuna jin dadinsa da sakamakon taron, yana mai cewa bayanan da aka gabatar sun nuna tasirin jarin da gwamnati da abokan hulda ke zubawa a bangaren ilimi.

Ya ce gudummawar hukumomin bada tallafi da sauran abokan hulda, tare da kokarin gwamnati, na taimakawa matuka wajen inganta ilimi a fadin jihar.
Gwamnan ya yaba da jajircewar abokan hulda wajen inganta koyarwa da koyo. Haka kuma ya ba su tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da aiki tare da su, da kuma samar da yanayi mai kyau da zai ba su damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta yi nazari kan dukkan shawarwari da gudummawar da aka bayar a taron, domin duba yiwuwar shigar da su cikin tsare-tsare da manufofin ilimi na jihar.
A nasa bangaren, Kwamishinan Ilimin Firamare, Dakta Lawal Yunusa Danzomo, ya bayyana cewa taron ya hada dukkan sassa da cibiyoyin da ke da alaka da tattara bayanan ilimi da kuma gudanar da ayyukan ilimi.
Ya jaddada cewa magance matsalolin bangaren ilimi na bukatar hadin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki.

Danzomo ya kara da cewa manufar shirin ita ce tabbatar da cewa kowanne yaro a Jigawa ya shiga makaranta, tare da wucewa zuwa mataki na gaba ba tare da yankewa ba.
Ya ce binciken da aka yi a baya-bayan nan ya nuna an samu ci gaba wajen shigar yara makaranta, da ci gaban karatunsu zuwa mataki na gaba da kuma yawan wadanda ke kammala karatu. Haka kuma an samu ci gaba wajen daukar malamai aiki, turasu wuraren aiki, horas da su, halartar aiki, da kuma ingancin koyarwarsu.
Taron na daga cikin kokarin Gwamna Umar Namadi na farfado da bangaren ilimi da kuma mayar da shi ginshikin ci gaban al’umma a Jihar Jigawa.
Daga cikin kungiyoyi da abokan hulda da suka halarci taron akwai PLANE, AGILE, UNICEF, Bankin Raya Kasashen Musulmi (IDB), da Save the Children, da sauransu.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
