Connect with us

Labarai

Majalisar Jigawa Ta Gargadi Dan Kwangila Kan Jinkirin Aikin Hanya a Kazaure

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Shugaban kwamatin ayyuka da sufuri na majalisar dokokin jihar Jigawa, Alhaji Yusuf Ahmad Bulangu ya bayyana rashin jin dadinsa bisa koma bayan da aikin hanyar burji ta Farun Daba zuwa Mai Tsani zuwa Ba Auzini zuwa Kafin Chiroma zuwa Gallu Babba zuwa Gallu Karama ke fuskanta a karamar hukumar Kazaure.

Shugaban  wanda ya bayyana rashin jin dadinsa lokacin da kwamatin ya ziyarci hanyar, ya bayyana koman bayan aikin ga rashin kudurin dan kwangilar na gudanar da aikin kamar yadda yakamata.

Alhaji Yusuf Ahmad Bulangu ya umarci sakataren kwamatin ya gayyaci manyan jami’an ma’aikatar ayyuka da dan kwangila da kwararre da ke kula da aikin hanyar domin tattaunawa akan wannan batu.

 

A nasa jawabin, injiniyan kamfanin dake aiki, injiniya Yusuf Na-Kano ya danganta jinkirin aikin ga rashin kasar ciko a mahadar dake kusa da farkon hanyar, yayin da tsakiyar hanyar su ka gamu da kasar laka maras kyau wadda za su kwashe domin maye gurbinta da kasa mai kyau dan samar da aiki mai inganci.

A nasa bangaren, kwararre da ke kula da aikin, injiniya Hassan Badamasi Kazaure, yace an bada kwangilar a watan Nuwambar 2024 domin kammalawa cikin shekara daya kuma ba a bin gwamnati bashin kudi.

Shi ma a nasa jawabin, wakilin ma’aikatar ayyuka da sufuri ta jihar jigawa, Injiniya Mustapha Usman, yace kamfanin ya rubuta neman karin wa’adin aikin domin samun damar cigaba da aikin hanyar.

Kwamatin ya kuma duba aikin gyaran hanyar Dandi zuwa Kazaure da aikin sabuwar hanyar Firji zuwa Guntai zuwa Buntusu zuwa Ba Auzini a karamar hukumar Gwiwa.

Labarai

Labarai2 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara