Labarai
Zamfara Ta Shirya Taron Horarwa na Makon Guda kan Shirin WASH
Hukumar Kula da Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Jihar Zamfara (LGSC) ta shirya wani taron horarwa na tsawon mako guda, wanda ya mayar da hankali kan kafa Sashen Ruwa, Tsafta da Lafiya – WASH), kamar yadda Gwamna Dauda Lawal ya amince, tare da batun ɗaga matsayin ma’aikatan hukumar zuwa manyan mukamai.
Sakataren Hukumar, Barista Shafi’u Bukhari, ne ya bayyana hakan a yayin taron, inda ya ce taron na da matuƙar muhimmanci domin ƙarfafa tsarin aiki da hukumomi, don tabbatar da kafa da gudanar da Sashen WASH yadda ya kamata, bisa ga amincewar da Gwamna Dauda Lawal ya bayar.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Jamilu Isah Gusau, ya fitar, ya bayyana cewa an shirya wannan mataki ne domin tabbatar da aiwatar da muhimman tsare-tsare ta hanyar samar da ayyukan ruwa, tsafta da lafiyar muhalli kai tsaye, tare da haɗin gwiwa da abokan hulɗa na cikin gida da na ƙasashen waje.
Ya ƙara da cewa dukkan ayyukan ruwa, tsafta da lafiyar muhalli na yankunan karkara a faɗin jihar, za su kasance ƙarƙashin kulawar wannan sashe, wanda aka ɗora masa alhakin gano, rubutawa, sa ido, da kula da duk kadarorin WASH na jihar a cikin ƙananan hukumomi daban-daban.
Barista Bukhari ya kuma bayyana cewa taron horarwar zai taimaka wajen ƙara ƙwarewa da ɗabi’ar aiki ga ma’aikata, tare da inganta ayyukan hidima ga al’umma a matakin ƙananan hukumomi.
Aminu Dalhatu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
