Labarai
Hajjin 2026: Jigawa Ta Kaddamar da Tawagar Likitoci da Za Su Kula Da Alhazai
Usman Mohammed Zaria
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta kaddamar da tawagar likitoci domin kula da lafiya da jin daɗin alhazai a yayin aikin Hajjin shekarar 2026.
A yayin bikin kaddamarwar da aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Dutse, Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya ce wannan shiri wani bangare ne na ci gaba da shirye-shiryen da hukumar ke yi domin tabbatar da aikin Hajji cikin natsuwa da lafiya ga dukkan maniyyata daga jihar.

A cewarsa, sabuwar tawagar da aka kaddamar na da alhakin gudanar da cikakken binciken lafiya ga dukkan maniyyata aikin Hajjin bana .
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce hukumar za ta dauki nauyin kudin gwajin lafiyar maniyyata gaba ɗaya, domin tabbatar da cewa sai waɗanda aka tabbatar sun dace da tafiya ne kawai za su tafi ƙasa mai tsarki.

Ya kara da cewa, tawagar za ta rika ba da kulawar lafiya da taimakon gaggawa ga alhazan jihar a duk tsawon zamansu a ƙasar Saudiyya.
Ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa goyon baya da jajircewarsa wajen kula da jin daɗin alhazan Jihar Jigawa.

Shugaban hukumar ya jaddada cewa, kaddamar da wannan tawagar likitoci muhimmin mataki ne wajen samun nasarar aikin Hajjin shekarar 2026 ba tare da tangarda ba.
A nasa jawabin, Shugaban Tawagar Likitoci kuma Babban Daraktan Asibitin Kwararru na Hadejia, Dokta Habibu Abubakar, ya tabbatar wa hukumar da al’umma cewa tawagar a shirye take ta gudanar da ayyukanta bisa kwazo da kwarewa.

Dokta Abubakar ya jaddada cewa tawagar, wadda ta kunshi kwararrun ma’aikatan lafiya, za ta yi aiki tukuru domin bin dukkan ka’idoji da dokokin lafiya, tare da ba da fifiko ga lafiya da walwalar alhazai bisa tsarin da aka tanada.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai24 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
