Labarai
Shugaban Hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed Ya Yi Murabus
Shugaban hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya NMDPRA, Ahmed Farouk.ya ajiye aikinsa.
Wata sanarwa daga fadar shugaban Najeriya ta ce tuni shugaba Tinubu ya aike da sunan mutumin da zai gaji Farouk Ahmed.
Sanarwar ta ce shugaba Bola Tinubu ya nemi majalisar dattawa da ta amince da naɗin Engineer Saidu Aliyu Mohammed a matsayin shugaban hukumar ta NMDPRA.
Shi ma shugaban hukumar NUPRC, Gbenga Komolafe ya sauka daga muƙaminsa, inda shi ma fadar shugaban ƙasar ta aike da sunan mutumin da zai gaje shi.
Wannan dai na zuwa ne kwana uku bayan da shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Aliko Dangote ya yi zargin cewa Farouk Ahmed na biya wa ƴaƴansa guda huɗu kuɗin makaranta a Switzerland da suka kai dala miliya biyar.
Tuni dai hukumar yaƙi da almundahana ta Najeriya ICPC ta ce za ta yi bincike kan zargin da shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya yi wa shugaban hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya NMDPRA, Ahmed Farouk.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
