Connect with us

Ilimi

Gidauniyar IRM ta Bada Tallafin Guraben Karatu ga Daliban Kiwon Lafiya 100 a Kaduna

Published

on

 

Daga Abdullahi Shettima

Gidauniyar IRM ta bayar da guraben karatu ga dalibai 100 na fannin Community Health, domin ƙarfafa ma’aikatan lafiya da inganta samun kulawar asali a yankunan da ba su da wadatattun hidimomi.

An gudanar da bikin bayar da guraben ne a yayin yaye dalibai na Aisha Ameer Healthcare Institute da ke Rigasa a Jihar Kaduna, inda iyaye, shugabanni na al’umma da jami’an ilimi suka hallara domin shaida wannan gagarumar gudunmawa.

Mai wakiltar Gidauniyar IRM, Alhaji Baba Sidi Kabir Mohammed, ya ce an kaddamar da shirin ne don tallafa wa matasa masu kishin aikin lafiya amma ke fuskantar ƙalubalen kuɗi da kan hana su ci gaba da karatu. Ya jaddada cewa gidauniyar ta daɗe tana mayar da hankali kan habaka jigon ɗan Adam, musamman a sashen kiwon lafiya.

A cewar gidauniyar, an zaɓi waɗanda suka ci gajiyar shirin ne bayan tantancewa bisa bajinta da kuma aniyar su ta mayar wa al’umma da ilimin da za su samu. Tallafin ya rufe kuɗin makaranta gaba ɗaya domin bai wa dalibai damar nutsuwa a karatunsu.

Mai magana da yawun gidauniyar ya ce, “Tallafa wa waɗannan matasa tamkar inganta rayuwar al’umma gaba ɗaya ne. Idan aka ba ɗalibai damar da suke nema, suna dawowa su yi aiki da jajircewa da gaskiya. Wannan shi ne hangen nesa na Gidauniyar IRM.”

Daraktan Aisha Ameer Healthcare Institute, Dr. Yahaya Balarabe, ya yabawa gidauniyar bisa wannan aiki na alheri tare da jinjina wa Wanda ya kafa ta, Hon. Ibrahim Rilwan Muhammad, bisa jajircewa wajen tallafa wa fannin lafiya da samar da ƙwararrun ma’aikata da za su yi aiki a matakai daban-daban na al’umma.

Haka nan, Hakimin Rigasa, Arc. Mohammed Aminu Idris, ya gode wa Gidauniyar IRM da mai kafawa bisa zaɓar Rigasa cikin yankunan da suka ci gajiyar shirin. Ya ce gudunmawar za ta taimaka ƙwarai wajen bunƙasa kula da lafiyar jama’a, musamman a unguwanni masu buƙatar ƙarin ma’aikata.

Daga cikin waɗanda suka ci gajiyar guraben, Fatima Abdul Salam, ta bayyana godiya a madadin sauran dalibai, inda ta ce tallafin ya rage wa iyalai nauyin da ya daɗe yana damunsu. Ta gode wa Hon. Ibrahim Rilwan Muhammad bisa ƙoƙarin da ya yi na buɗe wa matasa sabuwar hanya ta samun ilimi da cigaba.

Masu ruwa da tsaki a fannin lafiya sun yaba da wannan mataki, suna mai kira ga sauran kungiyoyi da masu hannu da shuni da su yi koyi da Gidauniyar IRM domin inganta kiwon lafiya a ƙasar nan.

Ana sa ran tallafin zai ƙara yawan ƙwararrun ma’aikatan Community Health da za su shiga aiki, abin da zai inganta ayyukan kiwon lafiya a matakin ƙauyuka da unguwanni.

 

Labarai

Labarai14 hours ago

Sauye-sauyen Da Tinubu Ya Samar Ya Haifar Da Cigaba A Jihohi – Namadi

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan da...

Labarai18 hours ago

Jigawa Ta Yi Nazarin Sabbin Tsare-tsaren Masaukin Alhazai A Saudiyya

Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce tana nazarin hanyoyin inganta jin daɗin alhazai...

Labarai2 days ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai3 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai3 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai3 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai3 days ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai3 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai4 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai4 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Mafi Shahara