Labarai
BUK Ta Horas Da Manoman Jigawa Kan Amfani Da Takin Gargajiya Don Inganta Gonaki
Daga Usman Muhammad Zaria
Cibiyar Binciken Wuraren Shuka ta Jami’ar Bayero Kano (Centre for Dryland Agriculture – CDA) tare da hadin gwiwar shirin inganta harkar noma na Soil Values, sun horas da manoman Jigawa kan yadda ake samar da takin gargajiya da kuma yadda ake amfani da shi domin farfado da ingancin ƙasa.
A yayin taron horas da manoma da aka gudanar a yankin Kunkuma na ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Dr. Bassam Abdulrahman ya bayyana cewa manufar shirin ita ce dawo da ƙimar ƙasar da ta lalace sakamakon dogon amfani da takin zamani.

Ya yi bayanin cewa ana samar da takin zamani ne daga sinadarai, kuma wasu daga cikin wadannan sinadarai na da haɗari, inda suke lalata ƙasar shuka sannu a hankali.
Dr. Abdulrahman ya kuma bayyana cewa cibiyar tare da hadin gwiwar shirin Soil Values ta horar da wasu manyan manoma (Lead Farmers) a Dutse, da Jahun, da Buji, da Kafin Hausa, da Birnin Kudu da Kiyawa kan yadda ake samar da takin gargajiya.

A cewarsa, an yi amfani da gonakin gwaji domin tabbatar da ingancin takin gargajiya, ta yadda manoma za su ga yadda takin ke mayar da sinadaran da ƙasa ta rasa bayan amfani da takin zamani iri-iri.
Shi ma a jawabinsa, Malam Mu’azu Salisu, ma’aikaci kuma malamin koyar da samar da takin gargajiya daga cibiyar, ya bayyana cewa sun yi samfurin gonar gwaji da nau’o’in taki daban-daban guda huɗu domin manoma su ga irin gagarumin tasirin takin gargajiya.

A nasa bangaren, Mataimakin Darakta na sashen bincike da kirkire-kirkire na CDA, Dr. Mustapha Bello, ya bayyana cewa an gudanar da taron horas da manoman ne domin nuna tsarin inganta kasar shuka domin samin yalwar yabayan kuma mai inganci.
Ya ce sun kafa gonar gwaji inda aka yi amfani da takin zamani iri daban daban a wani bangare, sannan aka yi amfani da takin gargajiya a wani bangaren, domin manoma su ga bambanci da cigaban amfanin gona da aka shuka lokaci guda da takin daban daban.

Dr. Bello ya shawarci manoma su yi amfani da ingantattun irin shuka hadi da takin gargajiya domin samun karin albarkar gona.
Wasu daga cikin manoman da aka horas, Bashir Bello daga Warwade a Dutse da Malam Amadu Mai unguwa daga Kukuma, sun bayyana farin cikinsu da sabbin ƙwarewar da suka samu tare da alkawarin fadada amfani da su domin ƙara yawan amfanin gona.
Sun yaba wa cibiyar saboda zaɓar al’ummar Kukuma domin gudanar da horon.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
