Labarai
Kungiyar Hadin Kai Ta Kafin Hausa Ta Horas Da Matasa 160 Sana’o’in Hannu
Daga Usman Mohammed Zaria
Gwamnatin jihar Jigawa ta sake jaddada kudirinta na cigaba da horas da matasa maza da mata sana’o’in hannu domin su kasance masu dogaro da kai.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan lokacin bikin yaye matasa 160 da suka sami horo akan sana’o’in dogaro da kai, wanda kungiyar hadin kai ta kafin Hausa ta gudanar.
Malam Umar Namadi ya bayyana cewar gwamnatin jihar ta bullo da shirye-shirye da nufin mayar da matasan jihar masu dogaro da kawunansu.

A don haka, Gwamnan ya godewa Kungiyar bisa bada horan, tare da yin kira ga matasan da suka amfana da shirin su yi amfani da ilmin da suka samu domin zama masu dogaro da kai.
A jawabinsa na marhabun ,Shugaban Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa Alhaji Abdullahi Nalayi ya nuna farin cikinsa bisa kokarin kungiyar na shirya bada horan tare da bada tabbacin ci gaba da tallafawa matasan yankin domin zama masu dogaro da kai.

Shima a nasa jawabin shugaban kungiyar kafin Hausa Unity Forum Malam Abdullahi Suleiman yace an zabo matasan ne daga mazabu goma sha daya na yankin.
Kazalika, an raba kayayyakin bunkasa tattalin arziki ga matasan da suka hada da kekunan dinki da na’u’rorin dafa abinci masu amfani da wuta da kayayyakin yin tiles da kuma kwamfutocin tafi da gidan ka.

Sauran sun hada da kayayyakin yin takalmi da na dinki da na yin jaka da na yin biredi da kayayyakin sanya solar da dai sauran su.
Haka kuma Gwamna Umar Namadi ya kai ziyarar bazata wuraren aikin gina makarantar Tsangaya da kuma makarantar kere kere ta gwamnatin jihar.

Namadi ya bayyana gamsuwa da yadda ayyukan ke gudana, tare da bukatar ‘yan kwangilar dake ayyukan da su kammala aikin akan lokaci kamar yadda aka tsara.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
