Ilimi
Gwamnan Neja Ya Halarci Jana’izar Marigayi Kaftin Baro.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago na daga cikin wadanda suka halarci sallar jana’izar Marigayi Kyaftin Hassan Mohammed Baro, Kwamishinan dindindin a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Neja.
Sallar jana’izar wadda aka gudanar a kusa da gidan marigayin da ke Minna ta samu halartar babban daraktan kula da harkokin addini Malam Umar Faruk Abdullahi wanda ya samu halartar jama’a da dama da suka hada da mai martaba Sarkin Agaie Alh Yusuf Nuhu.
Gwamnan ya kuma kasance cikin masu jajantawa a makabartar Musulmi ta Kpakungu inda aka yi jana’izar marigayi Captain Baro tare da babban limamin Minna, Malam Jibril Isah ya yi addu’ar Allah ya jikansa.
Daga karshe Umar Bago ya jagoranci tawagar jihar zuwa gidan marigayin da ke Brighter Area, Minna domin jajanta wa iyalan marigayin, ya kuma bukace su da su ci gaba da yin imani da Allah da kuma dage wajen yin addu’a ga marigayi Kaftin Baro.
Babban Limamin Minna, Mal. Jibril Isah da babban limamin Agaie, Mal. Ndanusa Ibrahim Yunusa ya yi addu’a ga mamacin.
Marigayi Captain Hassan Mohammed Baro ya rasu yana da shekaru 65 a duniya ya bar mata biyu da ‘ya’ya bakwai.
Har zuwa rasuwarsa, ya kasance kwamishinan dindindin a hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Neja, kuma ya taba zama shugaban karamar hukumar Agaie a karo na daya.
Ya kuma rike mukamin Darakta Janar Protocol na Gidan Gwamnati, a zamanin gwamnatin Dr. Mu’azu Babangida Aliyu.
ALIYU LAWAL.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai24 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
