Ilimi
Gwamnatin Zamfara Ta Koka Game Da Rashin Zuwan Likitoci Aiki A Babban Asibitin Jihar
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana damuwarta kan yadda likitoci ke kin zuwa aiki musamman a lokutan da suke kai ziyara wuraren kiwon lafiya da ba a shirya ba.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar, Suleiman Isah ya fitar, ya ce kwamishinan lafiya Dr. Nafisa Muhammad Maradun ta yi gargadi ga likitoci a babban asibitin garin Gusau, bayan da suka gano rashin zuwan su a wata ziyarar ba-zata.
Dakta Maradun, wadda ta kai ziyarar bazata asibitin, ta ce ta firgita da ganin cewa babu wani likita da ke bakin aiki, inda ta bayyana hakan a matsayin wani abu da ke faruwa a baya.
Ta yi Allah wadai da lamarin a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, ta kuma yi gargadin cewa, duk likitan da ba ya son bin ka’idojin kwararru da na gwamnati, ya kamata ya yi murabus maimakon kawo cikas ga tsarin kiwon lafiyar jihar.
“Idan ba za su iya yin biyayya ba, to su yi murabus, ko kuma su fuskanci sakamako daga gwamnatin jihar,” Kwamishinan ta yi gargadin.
Ta kuma jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakan ladabtarwa a kan ma’aikatan lafiya da ke yin kuskure ko wasa da aiki.
Dr Maradun ta jaddada cewa jin dadin marasa lafiya ya kasance babban fifikon gwamnati.
REL/AMINU DALHATU.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
