Ilimi
Abin Da Ya Sa Ba A Cika Satar Ɗalibai Ba A Borno — Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana riko da tsarin nan na “safe school initiative” a matsayin sirrin da ya sa ba cika samun labarin satar ‘yan makaranta ba a jihar.
Tsarin na “safe school initiative” dai wani shiri ne da ya wajabta gina katanga da daukar ma’aikata masu ɗauke da makamai domin kare lafiya da dukiya a makarantu.
Zulum ya bayyana ne Fadar Gwamnatin Najeriya jim kaɗan bayan fitowarsa daga wani taro na shuwagabanni a kasar nan.
Zulum ya ce “Mun kai akalla shekara bakwai zuwa takwas da ƙaddamar da tsarin ‘Safe School Initiative ’ a Jihar Borno.“Kusan duk makarantunmu na da katanga, mun gayyaci sojoji da ’yan sanda aikin tsare ɗalibai da makarantunmu.”
Zulum ya kara da cewa “Mun ɗauki ’yan banga da ’yan sa-kai suna taimaka wa jami’an tsaron kasar nan yadda ya kamata wurin tabbatar da tsaro a makarantun Jihar Borno.”
Gwamna Zulum ya jinjina wa jami’an tsaron bisa ƙoƙarin da ya ce suna yi wurin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Borno da sauran sassan kasar nan.
Jihar Borno dai ɗaya ce daga cikin jihohin da suka sha fama da bala’in ta’addancin kungiyar Boko Haram da ISIS masu tada ƙayar baya.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
