Ilimi
Karfafa Ilimi: EU Da UNICEF Sun Samar Da Sabon Tsari A Jigawa
Tarayyar Turai (EU) da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, tare da hadin gwiwar SUBEB sun ƙaddamar da gangamin wayar da kai kan sanya yara a makarantu a jihar Jigawa.
Shirin ya fara ne a kananan hukumomi bakwai na jihar da aka zaɓa a matsayin cibiyoyin da aka fara aiwatar da shirin.

Kwamitocin kula da makarantu (SBMCs) sun yaba da wannan ƙoƙari, inda suka bayyana cewa ya dace da lokacin da sabon zangon karatu ya fara.
A Jahun, Malam Ja’afar Danbaba ya ce shirin ya tara masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban, tare da bayyana musu muhimmancin da suke da shi wajen ɗaukar yara makaranta.


Shugaban SBMC na Birnin Kudu, Malam Ahmad Chiroma, ya yi kira da a tabbatar da dorewar shirin don ƙara shiga makarantu a jihar.
A Hadejia kuwa, Malam Aminu Hassan ya ce shirin ya kawo canji mai kyau, musamman da aka haɗa mata cikin tattaunawa kan ilimi.


Shi ma Malam Ali Babale na Kafin Hausa ya ce halartar jama’a gamgamin ya kayatar matuka, wanda ake sa ran zai haifar da Da mai ido.
Ya yi kira ga gwamnati da abokan hulɗa da su tabbatar da dorewar shirin zuwa tsawon lokaci.
Babale ya kuma nemi haɗin kan dukkan kananan hukumomi domin a samu ci gaba mai yawa a fannin ɗaukar yara makaranta.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
