Labarai
Najeriya Na Kara Samun Tagomashi Karkashin Mulkin Tinubu- Fadar Shugaban Kasa
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu ci gaba a fannoni daban-daban na tattalin arziƙi.
Sanarwar da mai ba Shugaban shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, ta ce ajiyar kuɗaɗen ƙasar na waje ya kai kusan Dala Biliyan 42 daga Dala Biliyan 32 da Tinubu ya tarar. Haka kuma gwamnati ta biya bashin sama da Dala Bliyan 7 ciki har da na kamfanonin jiragen sama.
Har ila yau, FFadar Shugaban Kasar ta musanta maganganun Atiku Abubakar na cewa yunwa da matsin tattalin arziƙi sun yi kamari, tana mai cewa kididdigar NBS ta nuna hauhawar farashi na raguwa tsawon watanni biyar, tare da samun ƙarin riba a harkokin kasuwanci.
Sanarwar ta ce gwamnati na ɗaukar matakan gyara kura-kuran baya, inda jihohi ke iya biyan albashi da fansho ba tare da jinkiri ba, kana kuma ana samun damar gudanar da ayyukan ci gaba.
Bayan shekaru biyu da watanni biyar kacal a ofis, gwamnatin yanzu ta bayyana alfahari da irin ci gaban da ake samu a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Daga Bello Wakili
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
