Ilimi
Rashin tsaro: Mai Martaba Sarkin Ilorin Ya Shirya Addu’a Ta Musamman
Mai Martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya bayyana kudurinsa na kara kaimi ga kokarin gwamnati wajen yaki da rashin tsaro da sauran munanan dabi’u a jihar.
Sarkin ya bayyana haka ne a fadarsa da ke Ilorin, a lokacin da yake addu’a ta musamman ga Allah Ya kawar mana da matsalar rashin tsaro da sauran matsalolin da ke tattare da hakan, a jihar.
Ya ce masarautar su za ta zama wata kakkarfar mai ba da kariya ga tabbatar da zaman lafiya da ake bukata a lungu da sako na jihar nan.
Alhaji Sulu-Gambari ya yabawa gwamnatoci a dukkan matakai bisa jajircewarsu wajen ganin an rage matsalolin tsaro zuwa mafi kankanta.
A nasa bangaren, babban limamin garin Ilorin, Imam Muhammad Bashir Solih, ya yi addu’ar Allah ya kara zaman lafiya, da zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.
Ya kuma yi kira ga mazauna jihar da ’yan Najeriya da su tallafa wa jami’an tsaro da sahihan bayanai kan ayyukan masu laifi domin daukar matakin gaggawa.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai24 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
