Ilimi
Gwamnatin Kwara Za Ta Horas Da Malamai Kan Dakile Shan Miyagun Kwayoyi A Tsakanin Ɗalibai
Gwamnatin jihar Kwara tare da hadin gwiwar Gidauniyar MTN, da Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya kan Yaki da Miyagun Ƙwayoyi (UNODC), da Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Kasa (NDLEA) za ta horar da shugabannin makarantu da malamai a wasu makarantun gwamnati don yaki da shan miyagun ƙwayoyi a tsakanin ɗaliban makarantu na firamare da sakandare a jihar.
Yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Ilori game da horon, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa matsalar shaye-shaye da jarabar miyagun ƙwayoyi na ƙara tsananta zuwa matakin mmakarantun firamare.
Gwamnan wanda mai ba shi Shawara na Musamman, Alhaji Sa’adu Salahu ya wakilta, ya ce an shirya taron ne da nufin samun goyon bayan malamai a dukkan matakai a fadin jihar, musamman a matakin ƙananan makarantu na firamare da sakandare.

Gwamna AbdulRazaq ya bayyana cewa wannan tattaunawa na da matuƙar muhimmanci a matsayin wani bangare na shirin gwamnati, na wayar da kan jama’a kan haɗarin shaye-shaye da suka dabaibaye al’umma, musamman a tsakanin matasa.
Ya ce za a mayar da hankali ne kan malamai a matsayin muhimman masu ruwa da tsaki, masu tsara ra’ayi, masu koyar da tarbiyya, kuma masu gina ɗalibai tun daga farko.
A nasa jawabin, Mataimakin Kwamandan NDLEA na Jihar, Jamilu Usman, ya bayyana nasarorin da hukumar ta samu wajen yaki da shan miyagun ƙwayoyi a jihar.
Ita ma a yayin zaman taron na musamman, wakiliya kuma mai horaswa daga Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya kan Yaki da Miyagun Ƙwayoyi (UNODC), Maria Ilugbuhi, ta ce malamai 30 da aka zaɓa a zagaye na farko, za su sami horo kan darussa 12 waɗanda suka shafi gina ƙwarewa, ƙara ilimi, ƙwarewar hulɗa da jama’a, yanke shawara, da sauran ƙwarewar zamantakewa.
ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
