Ilimi
Jigawa Za Ta Kashe Naira Biliyan Daya Domin Kula Da Lafiyar Mutane Masu Rauni
Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da biyan Naira Biliyan Daya domin ci gaba da bayar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga mutane masu rauni dubu 287 a faɗin jihar.
Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse, babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa, waɗanda za su ci gajiyar shirin sun haɗa da yara, mata masu juna biyu, marasa galihu, tsofaffi da kuma masu nakasa a ƙarƙashin shirin kula da lafiya na J-Basic Healthcare ga al’ummar da ke da rauni a fadin jihar.
Ya ƙara da cewa, majalisar ta kuma amince da ƙara yawan masu rijista daga 500 zuwa 1,000 a kowace mazaba.
A cewarsa, Asusun tallafin lafiya na jihar muhimmin sashi ne na shirin J-Health Basic Social Insurance, wanda aka ƙirƙira don kawar da cikas na kuɗi wajen samun lafiya ta hanyar ɗaukar nauyin kuɗaɗen hidimomi ga waɗanda ba za su iya biya ba.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana cewa, majalisar zartarwar ta amince da ƙarin alawus alawus na kowane wata ga masu amfana da shirin tallafin malaman makarantu na J-Teach su 1,100, daga ₦30,000 zuwa ₦40,000 a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin Gwamna Umar Namadi na ƙara wa malamai ƙwarin gwiwa, ƙarfafa aiki da inganta ilimi a fadin jihar.
Ya kuma bayyana cewa, amincewar ta biyo bayan buƙatar da ma’aikatar ilimi ta gaba da sakandare ta gabatar.
Sagir ya ce, majalisar ta amince da kashe sama da Naira Miliyan 134 domin biyan kuɗaɗen gudanarwa, harajin VAT, kuɗaden amincewa da guraben karatun dalibai, da kuɗin masauki ga ɗalibai 15 na zangon karatu na 2025/2026 a Jami’ar Near East da ke Cyprus.
Ya ƙara da cewa, majalisar ta kuma amince da kashe sama da Naira Miliyan 152 domin kuɗin alawus alawus na inshorar lafiya, kuɗin takardun biza, da na izinin zama, da na abinci da kuma sufuri.
Kwamishinan ya ƙara da cewa, jimillar adadin kuɗaɗen da majalisar ta amince da su domin ɗaliban 15 ya kai sama da Naira Miliyan 286.7 na zangon karatun 2025/2026.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai22 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
