Connect with us

Labarai

Gwamna Dauda Lawal Ya Amince Da Sabbin Nade-nade a Jihar Zamfara

Published

on

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da nadin sabbin jami’ai da suka hada da Manyan Mataimaka na Musamman, da Mambobin Kwamitoci, da Shugabannin Hukumomi da Ma’aikatun Gwamnati, domin ƙarfafa shugabanci da inganta gudanar da ayyuka a jihar.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da Mataimakin sa na Musamman kan Harkokin Yada Labarai, Sulaiman Ahmad Tudu, ya sanya wa hannu, inda ya bayyana cewa nade-naden sun fara aiki nan take.

A cewar sanarwar, an nada Aliyu Adamu Tsafe a matsayin Shugaban Hukumar kafafen sadarwa ta Zamfara, yayin da mambobin suka haɗa da Rufai Muhammad Anka, da Hassana Muhammad Bukkuyum, da Muhammad Tanko Khalil, da Yahaya Buhari Bungudu, da Adamu Sani Katuru, da kuma Idris Baba Shinkafi.

Haka kuma Kwamitin ya ƙunshi Kwamishinonin Ma’aikatun  yada labarai, da na Shari’a, da na ma’aikatar Kuɗi, da na Harkokin Ƙananan Hukumomi, da na ma’aikatar Kasuwanci, da na Harkokin Addini, sai Shugabar Hukumar Haraji ta Jihar, tare da Daraktan Hukumar Yada Labarai wanda zai kasance a matsayin Sakataren kwamitin.

Domin tabbatar da wakilci a fannoni daban-daban na siyasa a faɗin jihar, Gwamna Lawal ya amince da nadin Manyan Mataimaka na Musamman kan Harkokin Siyasa daga kowace mazabar Sanata guda uku, da suka hada da Nura Abdullahi Tsafe, da  Aminu Salmanu Shinkafi, da Nasiru Rabiu.

Haka kuma, Aisha Jamilu Dinawa ta samu mukamin Mataimakiyar Musamman kan Harkokin Yada Labarai, an kuma nada Salisu Isah a matsayin Babban Sakataren Hukumar Tallafawa Marasa Ƙarfi, yayin da aka nada Hassan Muhammad a matsayin Babban Sakataren Hukumar Wasanni ta Jihar Zamfara.

Bugu da ƙari, an nada Bilkisu Sani Makaranta a matsayin Sakatariyar Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Zamfara.

A wani bangare, Gwamna Lawal ya amince da sauya wurin aiki ga Amina Mustapha Ismail daga Hukumar Tsare-tsaren Finafinai ta Jihar zuwa Kamfanin Zuba Jari da Cigaban Kadarori na Zamfara a matsayin Babbar Darakta, an kuma umurce ta da ta mika ragamar hukumar ga babban darakta mafi girma kafin ta koma ga sabon mukaminta.

Gwamna Dauda Lawal ya taya wadanda aka nada murna, tare da yin kira gare  su da su  gudanar da ayyukansu bgaskiya da jajircewa, bisa ga tsarin ceto jihar da gwamnatin sa ta ɗauka.

 

Daga Aminu Dalhatu 

Labarai

Labarai2 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara