Labarai
Hukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Mayar Da Rarar Kudi Na Miliyoyin Naira Ga Gwamnati Da Alhazai
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa, ƙarƙashin jagorancin shugabanta Ahmed Umar Labbo, ta mayar da kudi sama da Naira Miliyan 31 ga mahajjata 930 da suka yi aikin Hajjin 2025 bayan Daular Saudiyya ta amince da rangwame a farashin dabbar hadaya da aka yanka wa mahajjatan jihar a Ƙasa Mai Tsarki.

An sami rangwamen a Aikin Hajjin 2025 wanda Sarkin Kazaure, Dakta Najib Hussaini Adamu ya jagoranta a matsayin Amirul Hajj na jihar, inda ya bayyana a rahotan da a bai wa Gwamna Namadi cewa, an tattaunawa tsakanin hukumar da kamfanin Hadaya wanda ya haifar da rangwamen sama da Naira Miliyan 31 ga mahajjata.

Ya ce za a raba kuɗaɗen ga mahajjatan, inda kowanne daga cikinsu da ya biya kuɗin hadaya ta hannun hukumar za a mayar masa da sama da Naira 42,000.

Dakta Najib Hussaini Adamu ya kuma bayyana cewa, hukumar ta sake mayar da kudi sama da Naira Miliyan 24, wanda rara ne daga kuɗaɗen da aka ware mata don gudanar da aiki.

Ya yaba wa hukumar mahajjata ta jihar da kuma Gwamna Namadi bisa kammala aikin Hajjin 2025 cikin nasara, tare da samar da ingantattun hidimomin jin daɗi ga mahajjata, musamman abinci, da masauki da kuma kula da lafiya.

A cewarsa, ba a samu rahoton ɓatan mahajjata ko haihuwar ɗa ba a bana, sannan ya yaba wa Gwamna bisa bai wa kowane mahajjaci daga jihar goron Sallah na kudi Saudiyya Riyal ɗari.

Ya ce sabon tsarin da hukumar ta kirkira na rarraba ɗakunan masauki ga mahajjata tun kafin isowarsu Makkah ya taimaka wajen magance matsalolin da aka saba fuskanta a baya.

A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya yaba wa Amirul Hajj da hukumar mahajjata bisa jajircewa da sadaukarwa da suka yi don tabbatar da nasarar aikin Hajjin 2025.

Ya kuma yaba wa hukumar bisa amfani da kuɗaɗen gudanar da aiki da aka ware mata bisa gaskiya da adalci, tare da kuma kulawar Amirul Hajj kan halin da mahajjatan jihar suka kasance a Makkah da Madinah.

A nasa jawabin, Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana cewa nasarorin aikin Hajji sun samu ne bisa goyon bayan da Gwamna Namadi ya bayar tun daga farko har zuwa ƙarshe.
Ya yi addu’ar Allah ya jagoranci Gwamna Namadi wajen tafiyar da al’amuran jihar.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
