Labarai
An Bukaci Gwamnatin Tarayya Da Na Jihohi Su Kafa Ma’aikatun Harkokin Iyali
An yi kira ga Gwamnatin tarayya da na jihohi da su kafa Ma’aikatu na Harkokin Iyali domin magance aikata laifuka da rushewar tarbiyya a ƙasar nan, wanda ake dangantawa da lalacewar abi’un iyali.
Limamin Masallacin Juma’a na Kofar Marusa da ke Katsina, Sheikh Nura Gwanda, ne ya yi wannan kira a cikin hudubar Juma’ar da ya gabatar mai taken “Iyaye da Tarbiyya a Matsayin Amanar Allah”.
Ya bayyana wasu daga cikin munanan dabi’u da suka bulla sakamakon rugujewar darajar iyali, da suka haɗa da shan miyagun ƙwayoyi, ta’addanci, fashi da makami, ‘yan daba, garkuwa da mutane da kuma rashawa a gwamnati da ma kamfanoni masu zaman kansu.
Sheikh Gwanda ya bayyana cewa mafi yawan ƙasashen Gabas ta Tsakiya da Turai suna da Ma’aikatu na Harkokin Iyali waɗanda ke kula da al’amurran aure, tarbiyyar yara, gado, cin zarafin iyali, cin zarafin yara, saki, kula da yara bayan rabuwar aure da sauran batutuwan iyali.
Ya jaddada cewa tunda iyali ne tubalin gina al’umma, kafa irin wannan ma’aikata a Najeriya zai taimaka matuƙa wajen shawo kan matsaloli irin su cin zarafin yara, zaman kashe wando, tabarbarewar tarbiyya da sauran munanan dabi’u musamman a arewacin ƙasar.
Liman ya ƙara da cewa kafa Ma’aikatar Harkokin Iyali zai kuma magance tushen matsalolin tsaro a ƙasar nan, duba da cewa mafi yawan masu aikata laifuka yara ne da aka yar da su ko kuma ‘ya’yan da iyayen su ba sa tare da juna.
Daga Isma’il Adamu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
