Connect with us

Labarai

ACF Ta Sha Alwashin Kwaicewa Tsoma Baki A Harkokin Siyasa

Published

on

Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta ja hankalin shugabanni da al’ummar Arewacin Najeriya da su kasance masu taka-tsan-tsan da hadin kai a yayin da ake fuskantar matsalolin tsaro, rikicin siyasa da bala’o’in muhalli da ke barazana ga zaman lafiya a yankin.

Shugaban Kungiyar, Cif Mamman Mike Osuman (SAN) ne ya yi wannan kira a ranar Alhamis a Kaduna, yayin taron kwamitin zartarwa na kasa karo na 78, inda ya gargadi shugabannin Arewa su guji sakaci da kuma yarda da labaran kanzon kurege.

Wannan ba lokacin ne da za mu zauna mu zuba ido ba. Ya zama wajibi mu kasance tsintsiya madaurinki daya wajen fuskantar rashin jituwa, son zuciya, shakku, yaudara, da jita-jita” In ji shi.

Ya ce Arewa ta dade tana fama da matsalolin tsaro daga ta’addanci zuwa ’yan fashi da kuma bala’o’in da suka shafi muhalli da suka hada da ambaliyar ruwa, da zaizayar kasa, yana mai bayyana cewa ACF na cikin damuwa matuka kan irin asarar rayuka da ake yi.

Shugaban ya kuma tuna da jerin fitattun shugabannin Arewa da aka rasa kwanan nan ciki har da tsohon Shugaban ACF, Cif Audu Ogbeh; da Sakatare Janar na biyu, Alhaji Umar Moriki, da tsohon Minista, Farfesa Jubril Aminu, da dattijo Alhaji Aminu Dantata, da tsohon Babban Alkalin Najeriya, Mai Shari’a Muhammad Uwais,  da kuma tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari.

Ya sake jaddada matsayin ACF na rashin tsoma baki a siyasa, inda ya bayyana cewa ko da yake mambobinta na da hakkin shiga  jam’iyyun siyasa daban-daban a matsayinsu na ‘yan kasa, amma kungiyar ba za ta taba jingina kanta da wata jam’iyya ba.

ACF ba ta da jam’iyya, kuma ba za ta taba kasancewa karkashin kowace jam’iyya ba. Abin da muke da shi kawai shi ne kishin Arewa da jama’arta, cikin mutunta hadin kan Najeriya,” in ji shi.

Osuman ya ce kungiyar za ta ci gaba da yin aiki tare da kungiyoyi masu irin wannan manufa, inda ya bayyana cewa Forum for National Restoration sun gayyace shi domin gabatar da jawabi a wurin taron su na kasa.

Dangane da shirye-shiryen gaba, ya sanar da cewa ACF na dab da kammala shiri domin bikin cika shekaru 25 da kafuwa, wanda aka tsara za a gudanar daga ranar 15 zuwa 30 ga watan Oktoban 2025.

An riga an kafa kwamitoci, kuma sun fara aiki. Na halarci wasu tarurrukan nasu, abin da suke yi lalle abin a yaba  ne.

Ya kuma gargadi mambobi su guji yada ra’ayoyi marasa tushe ko masu tsattsauran ra’ayi a dandalin sadarwa na ACF, yana mai cewa ya kamata su rika tuntubar  shugabannin jihohi ko kuma sakatariyar kungiyar.

Shugaban ya bayyana cewa ttaronna ACF karo na 78 ya kunshi batutuwa guda 12, ciki har da sabuntawa kan kamfanin ARECON da kuma batun “ETTE.” Ya ce kashi na goma na ajandar taro, wato State of the Nation, zai kasance karkashin jagorancin Jami’in Yada Labaran ACF, Farfesa Tukur Baba, wanda daga karshe za a fitar da sanarwa.

A karshe, Osuman ya yi kira ga ’yan Arewa da su kasance masu juriya, bin doka da oda da kuma hadin kai, yana mai cewa wannan lokaci ne na da yankin Arewa ke fuskantar kalubale daban daban.

Ya kuma jagoranci addu’ar neman gafara ga shugabanni da ’yan Arewa da suka riga mu gidan gaskiya.

Taron ya samu halartar manyan shugabannin Arewa, inda daga bisani suka shiga zaman taron sirri don tattaunawa game da  hadin kan al’ummar yankin Arewa, da  kalubalen tsaro da kuma shirin bikin cika shekaru 25 na kungiyar.

 

Daga Abdullahi Shettima 

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara