Labarai
Gwamna Namadi Ya Gargadi Shugabannin Hukumomi Su Guji Sayar Da Gandun Daji
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya gargadi shugabannin kananan hukumomi da su guji sayarwa da kuma raba makiyaya da gandun daji a yankunan su.
Ya yi wannan gargadi ne jim kadan da rantsar da sabon Shugaban karamar hukumar Gwaram da mataimakin sa a gidan gwamnati dake Dutse.
Malam Umar Namadi ya bayyana cewar shugabannin kananan hukumomi ba su da ikon sayarwa ko raba waɗannan wurare ba tare da izinin gwamnatin jihar ba.
Yana mai cewar gargadin ya zamo wajibi domin tabbatar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.
Namadi ya kuma shawarci sabon shugaban karamar hukumar ta Gwaram ya kasance mai tsoron Allah wajen gudanar da ayyukan sa tare da hada kai da kowa da kowa domin ci gaban yankin.

An rantsar da Alhaji Abdulkarim Musa Fagam a matsayin sabon shugaban karamar hukumar Gwaram da kuma Malam Nasiru Zubairu a matsayin sabon mataimakin shugaban karamar hukumar.
Kwamishinan shari’a na jihar, Barrister Bello Abdukadir Fanini ne ya rantsar da su.
Bikin ya samu halartar mataimakin Gwamnan jihar, Injiniya Aminu Usman da kakakin majalisar dokokin jihar jigawan, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin da wakilan majalissar zartarwa da dai sauran su.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
