Labarai
Gwamnatin Jigawa Ta Raba Naira Miliyan 50 Ga Mata Da Matasa
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya ce yaki da talauci muhimmin mataki ne na hanzarta ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
Ya bayyana haka ne a lokacin shirin gwamnatin jihar mai taken “Gwamnati da Jama’a” wanda aka gudanar a karamar hukumar Ringim.
Malam Umar Namadi ya jaddada muhimmancin horas da matasa sana’o’in hannu da samar da yanayin kasuwanci mai kyau domin cimma wadannan manufofi.

Saboda haka, ya yi kira ga zababbun wakilai, masu rike da mukaman siyasa, shugabannin kasuwanci da sauran attajirai da su taimaka wa al’ummarsu domin kara bunkasa ci gaba da habaka tattalin arziki.
A yayin taron, Kwamishinan jin kai da harkokin musamman na jihar, Auwal Danladi Sankara, ya raba naira miliyan 50 a matsayin tallafin karfafa gwiwa ga matasa da mata sama da 250.

A cewarsa, wannan shirin tallafin kudi na musamman an kirkiro shi ne domin tallafawa kokarin Gwamna Umar Namadi wajen samar da ayyukan yi ga matasa, kirkiro sabbin ayyuka da kuma rage talauci a jihar.
Ya kara da cewa, an tsara tallafin kudin ne domin wasu su fadada kasuwancinsu, yayin da wasu kuma za su fara sabon kasuwanci na zabinsu.

Ya ce kowanne daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin ya samu naira dubu dari biyu da hamsin (₦250,000), tare da yin alkawarin ci gaba da mara wa shirin manufofi 12 na Gwamna Namadi baya, wanda aka tsara domin tabbatar da arziki da ci gaba a Jihar Jigawa.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
