Labarai
Tinubu Ya Jinjinawa NAFDAC Bisa Matsayin Da Ta Taka A Hukumar Lafiya Ta Duniya
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) murna bisa ci gaba da riƙe matsayin Maturity Level 3 (ML3) na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wajen kula da magunguna da rigakafi.
Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa, an gudanar da binciken sake tantance matsayin WHO daga 28 zuwa 30 ga Mayu, 2025, inda aka kimanta NAFDAC bisa ka’idojin ƙasa da ƙasa.
Hukumar ta fara samun wannan matsayi na ML3 ne a 2022, inda ta zama hukumar farko a Afrika mai kula da ƙasashen da ba sa samar da magunguna da ta cimma wannan nasara.
Wannan sabon tantancewa ya biyo bayan wani binciken ne a watan Nuwamban 2024, tare da gudanar da tarukan duba Shirin Cigaban Cibiyoyi(IDP) guda biyar tsakanin Fabrairu zuwa Afriln 2025 domin tantance matakan gyara. WHO ta yaba wa NAFDAC kan ci gaba da samun tsari mai ƙarfi, da ke aiki yadda ya kamata, tare da yaba wa goyon bayan gwamnati wajen ƙarfafa hukumar.
Shugaba Tinubu ya jinjina wa shugabanni da ma’aikatan NAFDAC bisa ƙwarewa da sadaukarwa, yana mai cewa wannan nasara ta ƙara ɗaukaka matsayin Najeriya a fannin kula da lafiya da shirin kare cututtuka.
Ya ce wannan nasara na daidai da kudirin gwamnatinsa na Renewed Hope Agenda domin sauya tsarin kula da lafiya.
Shugaban ya yi nuni da ci gaba da ake samu, ciki har da inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 17,000, kyautata kulawa da mata masu juna biyu da na’urorin gano cututtuka a yankunan da ba su da iisassun kayayyakin kula da lafiya, horar da ma’aikatan lafiya 120,000, da kuma ninka yawan masu amfani da shirin inshorar lafiya na ƙasa cikin shekaru uku.
Ya kuma tabbatar da aniyarsa ta ƙarfafa samar da kayayyakin kiwon lafiya a cikin gida da jawo ra’ayin masu zuba jari a fannin lafiya.
Tinubu ya yi alkawarin ci gaba da tallafa wa NAFDAC a yunkurinta na cimma matsayin WHO Maturity Level 4, mafi girma a duniya kan ingancin sarin kula da magunguna.
Daga Bello Wakili
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
