Ilimi
An Fara Yiwa Maniyatan Aikin Hajjin Bana Bita a Kaduna

Hukumar kula da aikin hajji ta jihar Kaduna ta kaddamar shirin ilmamtarda maniyatan aikin hajjin bana da ya zama wajibi ga kowane maniyaci ya halarta.
Mai magana da yawun hukumar alhazan Yunusa Muhammad Abdullahi ya bayyana cewa ana gudanar da bitar asabar da lahadi na kowane mako, kuma a dukkanin kananan Hukumomin jihar Kaduna 23.
A sakon da shugaban hukumar alhazan na jihar Kaduna Malam. SALIHU S. Abubakar ya aika dashi wajen taron bitar, yayi bayanin cewa, manufar Shirin ita ce tabbatar da cewa an ilmantar da maniyatan yadda zasu sauke faralinsu.
An dai dauko kwarrun malamai da aka dorawa alhakin gabatar da wannan bita ga maniyatan bana na jihar Kaduna.
Safiya Abdulkadir
S
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai22 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
