Labarai
Jihar Jigawa Ta Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Ga Marigayi Muhammadu Buhari
Majalisar Dokokin jihar Jigawa ta gudanar da addu’oi na musamman ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda aka yi jana’izar sa a mahaifar sa dake garin Daura na jihar Katsina.
An gudanar da addu’oin ne a lokacin zaman majalisar na Laraba bisa umarnin Shugaban majalisar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin.
Wakilin mazabar Maigatari, Alhaji Habu Muhammad, Wanda ya jagoranci gabatar da addu’oin ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya gafartawa marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari Ya Kuma yafe masa kurakurensa, tare da fatan Aljanna ta zamto makomar sa.
Alhaji Habu Muhammad Wanda ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga Najeriya, ya yi addu’ar Allah Ya baiwa al’ummar jihar Katsina da Kuma iyalansa, da ma kasa baki daya hakurin jure wannan babban rashi.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
