Labarai
Al’umma Na Ci Gaba Da Kai Ziyarar Ta’aziyya Garin Daura
‘Yan Najeriya daga sassa daban-daban na ci gaba da nuna alhini da yin ta’aziyya bisa rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda aka yi jana’izarsa jiya a Daura.
A wajen addu’ar rana ta uku da aka gudanar a gidan marigayin da ke Daura, malamai da limamai daban-daban sun gudanar da addu’o’i domin roƙon rahamar Allah ga marigayi shugaban ƙasa.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya wakilci Gwamnatin Tarayya wajen karɓar gaisuwar ta’aziyya, yayin da Gwamna Dikko Radda ya wakilci Gwamnatin Jihar Katsina, sai kuma Maman Daura, ɗan uwa ga marigayin, ya karɓi ta’aziyya a madadin dangin mamacin.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun kasance cikin wadanda suka halarci zaman addu’ar.

Haka zalika, akwai sanatoci da ‘yan majalisa na da, da na yanzu, ministoci, jakadu, tsofaffin gwamnoni, sarakuna da ‘yan kasuwa maza da mata da suka yi ta’aziyya ga marigayi Muhammadu Buhari.
A wani bangaren kuma, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya sanar cewa a gobe Alhamis ne za a kammala zaman makokin a hukumunce.

Shettima ya bayyana cewa hakan zai kasance ƙarshen aikin tawagar shugaban ƙasa, inda za su koma Abuja, yayin da iyalan marigayin da kuma Gwamnatin Jihar Katsina za su ci gaba da karɓar masu zuwa ta’aziyya.
Daga Isma’il Adamu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
