Labarai
Tsananin Zafin Rana Tsakanin Kasashen Africa
Sudan ta Kudu da Kenya da Senegal da Mali sun fitar da sanarwar gargaɗi kan matsanancin zafi yayin da yanayin zafin da aka alaƙanta da ɗumamar yanayi ya bazu a yankunan Afirka.
Sudan ta Kudu ta rufe makarantu domin kare yara yayin da ake sa ran yanayin zai kasi maki 45 a ma\aunin salshiyos.
A Kenya, hukumar kula da yanayi a ƙasar ta gargaɗi yankunan da ke arewaci kan cewa za su fuskanci matsalar zafi da ta zarce digiri 30 kan ma’aunin salshiyos daga yau zuwa kwanaki 10 masu zuwa.
An samu irin wannan yanayi na zafi a Senegal inda aka yi fama da matsanancin zafin na tsawon kwanaki a faɗin ƙasar kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Dakaractu ta ruwaito.
Hukumar kula da yanayi ta Senegal ta ce yanayin zai kai tsakanin digiri 44 da 45 a kan ma’aunin salshiyos musamman a yankin kudu maso gabashin ƙasar. Yayin da yankin tsakiya da kudu maso yamma za su kasance cikin yanayin zafin da ya haura maki 42 a ma’aunin salshiyos.
A Mali ma, tsakiyar Bankass Circle da ke yankin Mopti ta sake nazarin jadawalin karatun makarantu a yanayin zafin, in ji kafar yaɗa labarai mai zaman kanta, Studio Tamani.
Matsanancin zafin a gabashin Afirka dai an alaƙanta shi da yanayin El Nino da ke yawan faruwa idan koguna suka yi zafi kuma suka gangaro kan ƙasa a gaɓar ruwan Amurka ta kudu kuma ya afka cikin koguna.
-
Labarai7 days ago
Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Tarakta 300 Ga Manoma Daga Amurka
-
Labarai21 hours ago
NAHCON Ta Jinjinawa Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Bisa Shirye-shiryen Hajjin Bana
-
Ilimi5 days ago
Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Gidaje A Jami’ar Tarayya Da Ke Babura
-
Labarai21 hours ago
Amurka Ta Dakatar Da Kudurin Kai Jirgin Bama-Bamai Zuwa Isra’ila
-
Labarai6 days ago
An Samar Da Sabon Tsari Da Zai Inganta Harkar Noman Rogo A Najeriya
-
Fasaha2 days ago
Kusan Malaman Makaranta Dubu 2 Ke Samun Horo a Barno
-
Kasuwanci2 days ago
CBN Ya Bai Wa Masu POS Wa’adin Yin Rajista Da Gwamnati
-
Fasaha2 days ago
Bankuna Za Su Fara Cirar 0.5% Daga Masu Tura Kudi Ta Intanet