Labarai
An Kama Mutane Da Dama A Los Angeles Bayan Sanya Dokar Hana Fitar Dare
‘Yan Sanda a birnin Los Angeles da ke Amurka sun ce sun yi nasarar kama mutane da dama, bayan da aka shiga rana ta biyar ana zanga-zangar nuna adawa da kamen bakin haure da gwamnatin Donald Trump ke yi.
Har yanzu dai ana ci gaba da farautar baƙin haure a yankin, duk kuwa da zanga-zangar adawa da matakin da aka faro a ranar Juma’ar da ta gabata, inda a yanzu aka tura dakarun tsaro don ba da kariya ga jami’an shigi da fici su samu damar gudanar da ayyukansu.
Wannan mataki dai ya haifar da musayar yawu tsakanin hukumomin jihar da kuma Trump, duk da cewa ya sha alwashin ci gaba da aiwatar da ƙudurinsa, matakin da ya sanya gwamnan jihar ta Califonia Gavin Newsom, ya zargin shi da yi wa dimodaraɗiyya karan tsaye.
A jiya Talata ne dai Trump ya kare matakinsa na tura dakaru dubu 4 da sojojin ruwa 700 yankin na Los Angeles, ya na mai cewa ya yi hakan ne don dakatar da maƙiyan mamaye birnin.
Dakarun dai basu da ikon yin kame, aikinsu shi ne tabbatar da tsaron jami’an da ke gudanar da kamen da kuma kayayyakin gwamnati.
Magajiyar garin Los Angeles, Karen Bass ta sanya dokar hana fita a daren jiya da kuma safiyar yau Laraba a wani yanki na birnin, inda ta ce an ɗauki matakin ne sakamakon yadda ake fasha shaguna da kuma sace kayayyaki.
Bayan sanya dokar hana fitar da ta fara aiki daga ƙarfe 2 na daren jiya agogon Amurka, ƴansanda sun kutsa yankuna da dama, inda suke harba alburushin roba don tarwatsa masu zanga-zangar.
rfi
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
