Labarai
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ya Nemi Hadin Kan Al’ummar Jihar
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman ya bi sahun sauran al’ummar Musulmi ta duniya domin bikin murnar babbar Sallah.
A jawabinsa da safiyar ranar Sallah, shugaban majalisar ya yi godiya ga Allah Maɗaukaki bisa damar da ya ba shi da sauran al’umma na ganin wannan rana.
Ya jaddada darussan da ke cikin biyayya da ƙaunar Allah kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) da dansa Annabi Isma’il (AS) suka nuna, inda ya bukaci Musulmi da su rungumi dabi’un ƙauna, tausayi, da haɗin kai a wannan lokaci.
Rt. Hon. Liman ya kuma bukaci jama’ar Jihar Kaduna da su ci gaba da goyon bayan gwamnatin Gwamna Uba Sani, inda ya yaba da jajircewar gwamnan wajen ci gaban jihar.
Ya yi addu’ar neman zaman lafiya, da haɗin kai a fadin Najeriya, tare da yin addu’a ta musamman ga mahajjatan da ke gudanar da aikin Hajji, yana rokon Allah ya karɓi ibadunsu kuma ya dawo da su gida lafiya.
Kakakin Majalisar ya kammala da cewa: “Eid Mubarak ga daukacin al’ummar Musulmi, tare fatan Allah ya sa wannan lokaci ya kawo zaman lafiya da albarka a gidajenmu da ma ƙasa baki daya.” in ji shi.
Tun da farko yayin gabatar da hudubar sallar idi, Babban Limamin Masallacin Makera Central, Sheikh Jibril Ibrahim Maihanji, ya shawarci Musulmi da su kiyaye koyarwar addinin Musulunci bisa dokokin da aka shimfida domin samun dacewa.
Sheikh Jibril Maihanji ya yi amfani da hudubar wajen kiran gwamnati a dukkan matakai da su samar da ayyukan yi ga matasa da dama a cikin ƙasa, a matsayin hanyar magance miyagun dabi’u da laifuka.
Babban Limamin ya kuma shawarci matasa da su nemi ilimin zamani tare da na addini, sannan su koyi sana’o’i domin su zama masu amfani ga al’umma.
Sallar Idin ta samu halartar daruruwan Musulmi daga Makera da kewaye.
Shamsuddeen Mannir Atiku
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai22 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
