Kasuwanci
Gwamna Abdulrazaq Ya Yi Alkawarin Ci Gaba Da Aikin A Kwara
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen gina jihar da ma’aikata za su bunkasa, samar da ayyukan yi masu nagarta, da baiwa kowane bangare damar bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban jihar.
Gwamna AbdulRazaq a cikin sakonsa na bikin ranar ma’aikata ta duniya na shekarar 2025, a Ilorin, ya mika sakon gaisuwa ga maza da mata da jama’a da kungiyoyi masu zaman kansu wadanda kokarinsu ke karfafa tattalin arziki da samar da makomar al’ummarmu.
Ya yaba da gagarumar gudunmawar da ma’aikata ke bayarwa a kowane fanni na sadaukarwa, juriya, da fasaha wanda ya sa su zama ginshiƙan girma da ci gaba.
Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatin na aiwatar da manufofin da za su karfafa ma’aikatan gwamnati, da bunkasa tattalin arziki, da jawo jari, da fadada ayyukan yi.
Ya bayyana cewa, ta hanyar tsare-tsare na samar da ababen more rayuwa da na zamantakewar al’umma, gwamnatin ta tabbatar da daidaiton harkokin kudi, da tabbatar da biyan albashi a kan kari, da tallafa wa harkokin kasuwanci, da samar da hanyoyin kare lafiyar jama’a.
Gwamna AbdulRazaq ya bukaci ma’aikata da su rungumi canji, su inganta nagarta, da kuma yin shiri domin samun damar gobe.
“Ina mika godiya ta ga dukkan ma’aikata saboda muhimmiyar rawar da suka taka a cikin nasarorin da muka samu. Ina kuma yaba wa shugabannin mu na Labour saboda goyon baya da hadin gwiwa.” Ya ce
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
