Kasuwanci
Kwamitin Gudanar da Kasuwa Maras Shinge Ta Maigatari Sun Ziyarci Fadar Gumel
Masarautar Gumel ta ce za ta bayar da dukkan goyon baya da hadin kai da ake bukata domin ci gaban yankin kasuwancin da ba shida shinge na Maigatari a jihar Jigawa.
Mai Martaba Sarkin Gumel Alhaji Ahmad Mohammad Sani ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin Jiha mai kula da shiyyar fitar da kaya ko kasuwanci maras shinge na Maigatari a fadar sa.
Ya ce, nan ba da dadewa ba majalisar masarautar za ta shirya taro da hakiman Gundumomi da Unguwanni da Kauyuka domin fadakar da al’ummarsu kan gudunmawar da suke bukata domin samun nasarar wannan yankin.
Sarkin wanda ya samu wakilcin Dallatun Gumel, Alhaji Musa Ayuba ya ce aikin noman rani da asibitin kashi da cibiyar dialysis da gwamnatin Malam Umar Namadi ta kafa a Gumel ayyuka ne da ke yin tasiri kai tsaye ga rayuwar al’ummar yankin.
Tun da farko shugaban kwamitin kula da shiyyar fitar da kaya da babu haraji ko shinge na jiha kuma kwamishinan kasafin kudi da kididdiga Alhaji Babangida Umar Gantsa ya ce sun je fadar sarkin ne domin sanar da shi irin nasarorin da aka samu tare da neman hadin kan sa da addu’o’i na uba.
Gantsa, ya kara da cewa gwamnati ta kashe makudan kudade wajen samun Amincewa da Lasisi domin sanya Maigatari fa matsayin wata kasuwa ko yanki da za a yi cinikayya maras shinge ko haraji don bunkasar Jihar Jigawa da kasa baki daya.
Shima da yake nasa jawabin Hakimin Gumel Arewa, Alhaji Sani Abdullahi Babandi ya yi kira ga ‘yan kwamitin da su tuntubi hukumomin da abin ya shafa don gyara hanyar gwamnatin tarayya da ta hada Gumel zuwa Maigatari domin samun damar shiga yankin cikin kwanciyar hankali.
USMAN MZ
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
