Connect with us

Kasuwanci

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda a Sambisa da Kudancin Tumbun

Published

on

Rundunar sojin sama na Operation Hadin Kai ta yi nasarar aiwatar da wasu hare-hare ta sama guda biyu, inda ta auka wa maboyar ‘yan ta’adda a yankin Sambisa na jihar Borno da kuma Kudancin Tumbun.

 

A wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar, ya ce harin farko ya afku ne da misalin karfe 5:30 na safe a Kollaram- sanannar tungar ‘yan tada kayar baya, a ranar 15 ga watan Afrilu, inda aka kawar da mayaka da dama tare da lalata muhimman ababen more rayuwarsu.

 

Farmaki na biyu kuwa ya biyo bayan da misalin karfe 3:55 na rana a garin Arra na Sambisa, bayan binciken sirri da bincike da aka gudanar a baya an gano tarin ‘yan ta’addan, kuma hotunan da aka gani a zahiri sun tabbatar da kasancewar su. An yi amfani da ingantattun alburusai, wanda ya haifar gagarumar nasara da kuma kawo cikas ga ayyukan kungiyar.

 

A cewar sanarwar, wadannan ayyuka na baya-bayan nan wani bangare ne na ci gaba da yakin da aka tsara domin lalata karfin ‘yan ta’adda, da ruguza tsarin shugabancinsu da kuma kawar da mafakarsu a fadin Nijeriya.

 

PR/Usman Sani.

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara