Connect with us

Labarai

Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Bukaci Taimakon NAMA Don Gudanar Da Aikin Hajjin Bana Cikin Nasara 

Published

on

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta bukaci Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA) ta ci gaba da ba da goyon baya domin tabbatar da nasarar gudanar da aikin Hajjin bana.

 

Shugaban Hukumar Alhazan Malam Salihu Abubakar ne ya yi kiran, yayin ziyarar aiki ga jami’an NAMA a filin jirgin sama na Hassan Usman Katsina  da ke Kaduan.

 

Malam Salihu Abubakar, wanda sakataren gudanarwar hukumar Malam Baba Muhammad Rufa’i ya wakilta, ya yaba  wa NAMA bisa gudunmuwar da take badawa wajen nasarar aikin Hajji akoda yaushe, inda ya roƙi irin wannan haɗin gwiwa a bana.

 

Ya jaddada muhimmancin samun ingantattun hanyoyin sufuri, tare da yin kira ga hukumar ta NAMA, da ta tabbatar da samar da duk wasu kayan aiki da ake bukata domin kauce wa cikas yayin jigilar alhazai.

 

A nasa jawabin, Manajan Harkokin Zirga-zirgar Jiragen Sama na filin jirgin, Alhaji AbdulMajid Mohammed, ya tabbatar da aniyar NAMA na ci gaba da tallafa wa aikin jigilar alhazan Jihar Kaduna.

 

Ya bayyana cewar har yanzu akwai matsalar ginin sabuwar hasumiyar kula da zirga-zirga da ba a kammala ba, yana mai  cewa yawan katsewar wutar lantarki na kawo cikas, wanda ya sa yanzu filin jirgin na aiki ne zuwa ƙarfe 5 na yamma.

 

Duk da waɗannan ƙalubalen, Alhaji AbdulMajid ya tabbatar wa Hukumar Jin Daɗin Alhazai cewa NAMA na da burin  ganin cewa aikin jigilar alhazan Kaduna zai kasance cikin tsari da kwanciyar hankali.

 

Ya tabbatar da cewa ana ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin rage yiwuwar samun cikas da kuma tabbatar da nasarar tafiyar Hajjin bana.

 

Rel/Adamu Yusuf

Labarai

Labarai24 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara