Ilimi
An Yi Kira Ga Al’ummar Musulmi Da Su Kara Yawan ‘Ya’yan Itatuwa Da Sha A Ramadan
An yi kira ga al’ummar musulmi da su kara yawan ruwa da ‘ya’yan itatuwa a lokacin azumin watan Ramadan domin inganta sinadaran jiki.
Wani kwararre a fannin lafiya a Jami’ar Ilorin, Farfesa AbdulRahman Afolabi ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Ilorin, jihar Kwara.
Ya ce a lokacin azumi da ake tsananin zafi a hankali ruwan jiki yana raguwa.
A cewarsa karuwar cin ‘ya’yan itatuwa daban-daban zai yi matukar amfani ga musulmi mai azumi.
Farfesa Afolabi ya bayyana cewa a lokacin azumin watan Ramadan musulmi sun kaurace wa abinci da abin sha, tare da hana jikinsu cin abinci da suka saba.
Ya ba da shawarar a kara amfani da ‘ya’yan itatuwa irin su kankana, karas, da lemu domin dawo da abin da jiki ya rasa.
Farfesa Afolabi ya ci gaba da cewa sanya ‘ya’yan itatuwa a cikin abincinmu na iya samar da kuzari, da sinadirai masu mahimmanci, da kuma samar da ruwa don kiyaye jiki da kuzari a lokacin azumin Ramadan.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
