Labarai
Shugaban Hafsan Sojan Sama Na Najeriya Ya Zama Shugaban Kungiyar Sojojin Sama Na Afrika
Shugaban Hafsan Sojan Sama, Air Marshal Hasan Abubakar ya zama Shugaban Kungiyar Sojojin Sama na Afrika-AAAF.
Da yake jawabi a wajen taron shugabannin sojojin saman Afrika da aka gudanar a kasar Zambiya, Air Marshal Hasan Abubakar, ya jadadda bukatar samar da hanyoyin warware kalubalen tsaro da kasashen Afirka ke fuskanta.
A cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa, ya fitar, hafsan hafsoshin ya bayyana muhimmancin hadin gwiwa tsakanin shiyya da dabarun hadin gwiwa wajen karfafa karfin jiragen na Afrika da kuma magance barazanar da ake fuskanta.
Ya jaddada cewa, inganta hadin gwiwa tsakanin sojojin saman Afrika na da matukar muhimmanci wajen tunkarar kalubalen tsaro da ke kunno kai kamar ta’addanci, tada kayar baya da kuma laifuffukan kasa da kasa.
Air Marshal Hasan Abubakar ya lura da cewa taron na nuni ne da jajircewa wajen tabbatar da tsaro, kwanciyar hankali da wadata a Afirka.
Ya yi kira da a sabunta alkawari daga dukkan mambobin, yana mai jaddada cewa hadin kai na da matukar muhimmanci wajen cimma manufofin kungiyar.
A cewar sanarwar, kungiyar ta AAAF, kungiya ce mai zaman kanta da ba ta siyasa ba, da ta himmatu wajen inganta karfin samar da kariyarar sararin samaniyar Africa da hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka.
PR/Usman Sani.
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
