Labarai
‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Tsohon Darakta Janar Na Hukumar NYSC
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Tsiga da ke karamar hukumar Bakori a jihar Katsina inda suka yi garkuwa da tsohon Darakta Janar na Hukumar Kula da Matasa masu yi wa kasa hidima NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya da wasu mutum takwas.
Majiya mai tushe ta bayyana hakan ga gidan rediyon Najeriya a wata hira da manema labarai, yayin da ‘yan sanda ba su tabbatar da faruwar lamarin ba.
Wani shaidan gani da ido ya bayyana yadda gungun ‘yan bindigan suka afkawa al’ummar a kan babura da misalin karfe sha biyu na dare.
“Da misalin karfe 12 na dare ne ‘yan bindigar suka shigo garin na tsiga a bisa babura, inda suka rika harbi a sararin samaniya, sannan suka nufi gidajen da suka kai hari.”
“Kimanin mutum goma daga cikin ‘yan bindigar ne suka kai farmaki gidan Birgediya Janar Maharazu Tsiga, yayin da ssauran suka bazama wasu gidajen, inda suka tasa keyar mutum takwas.” inji shi.
Wakilinmu ya ruwaito cewa ‘yan bindiga sun sha kai wa al’ummar Tsiga hari a cikin shekaru bakwai da suka wuce.
Daga Isma’il Adamu
-
Ilimi7 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai2 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai2 days ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
