Ilimi
Gidan Rediyon Najeriya Kaduna Ya Je Ta’aziyar Albabello
Mahukunta gidan Radiyon tarayya na kaduna sun kai wa iyalan Alhaji Bala Albabello ta”aziya wanda Allah ya yi wa rasuwa ranar litini 3 ga watan fabrairu na shekarar 2025.
Shugaban gidan Radion, Malam Buhari Awwalu ne ya jagoranci tawagar zuwa gidan marigayin dake Tudun Jukun a zaria.
Malam Buhari Awwalu ya jajantawa iyalan marigayin,inda ya yi addu’ar Allah ya bai iyalan hakurin rashin sa,kuma ya sa a rinka tunawa da kyawawan dabi’un sa na taimakawa marasa karfi da kuma Dora al’umma akan turbar kasuwanci.
Ya kuma roki Allah da ya sanya shi a aljannar firdausi.
Da ya ke jawabi a masadin iyalan,Alhaji Hassan Abdulwahab ya yi bayanin cewa marigayi Albabello ya sadaukar da rayuwar sa ce wajen hidimtawa al’umma.
Cikin mahukunta gidan Radion da suka rufa wa shugaban bayan sun hada mataimakin darakta mai kula da sashin mulki,Malam umar Alkali da mataimakin darakta mai kula da sashin shirye-shirye,Malam Idris Yahaya da mataimakin darakta mai kula da sashin talace-talace, Malam Musa Yahaya da mataimakin darakta mai kula da sashin cinikayya,Malam Abubakar Lawal Dutsen ma,da mataimakin darakta mai kula da wasanni da watsa shirye-shirye daga nesa,Malam Lawal Ali Garba da mai rikon shugaban sashin sabuwar hanyar yana labarai na zamani, Malam Umar usman Tsiga da shugaban sashin kula da na’urorin kwsmfuta,Malam Nasiru Umar chawai da mai binciken kudi,Malam Yusha’u Umar.
HALIRU HAMZA
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
