Connect with us

Labarai

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Tsohon Darakta Janar Na Hukumar NYSC

Published

on

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Tsiga da ke karamar hukumar Bakori a jihar Katsina inda suka yi garkuwa da tsohon Darakta Janar na Hukumar Kula da Matasa masu yi wa kasa hidima  NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya da wasu mutum takwas.

Majiya mai tushe ta bayyana hakan ga gidan rediyon Najeriya a wata hira da manema labarai, yayin da ‘yan sanda ba su tabbatar da faruwar lamarin ba.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana yadda gungun  ‘yan bindigan  suka afkawa al’ummar a kan babura da misalin karfe sha biyu na dare.

Da misalin karfe 12 na dare ne ‘yan bindigar suka shigo garin na tsiga a bisa babura, inda suka rika harbi a sararin samaniya, sannan suka nufi gidajen da suka kai hari.

Kimanin mutum goma daga cikin ‘yan bindigar ne suka kai farmaki gidan Birgediya Janar Maharazu Tsiga, yayin da ssauran suka bazama wasu gidajen, inda suka tasa keyar mutum takwas.” inji shi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa ‘yan bindiga sun sha kai wa al’ummar Tsiga hari a cikin shekaru bakwai da suka wuce.

Daga Isma’il Adamu

Labarai

Labarai16 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai18 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai7 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara