Kasuwanci
‘Yan Sanda Sun Mika Bakin Haure 165 A Birnin Kebbi
Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ta kama wasu bakin haure 165 da aka ce sun fito ne daga kasashen da ke amfani da harshen Faransanci tare da mika su ga hukumar kula da shige da fice ta kasa dake jihar domin gudanar da bincike.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar ya fitar kuma ya mika wa gidan rediyon Najeriya a jihar Kebbi, ya ce, bisa rahoton bayanan sirri, an gano sama da mutum dari biyu a wani gida mai dakuna uku da ke unguwar Kuwait a cikin birnin Birnin Kebbi.
Sanarwar ta ce, tawagar jami’an ‘yan sanda da ke sashin binciken manyan laifuka (SCID) ne suka kai samame unguwar inda suka yi nasarar cafke mutane dari da sittin da biyar (165).
Ya bayyana cewa, yayin da ake gudanar da bincike, an gano cewa, dukkan wadanda ake zargin sun fito ne daga kasashen da Faransa ta yiwa mulkin mallaka da suka hada da Burkina Faso, Jamhuriyar Benin, Jamhuriyar Nijar, Mali da Ivory Coast.
A cewar sanarwar, bincike ya kara nuna cewa, wadanda ake zargin suna zaune ne a Najeriya ba tare da wasu takardu masu inganci ba kuma ana zarginsu da hannu a cikin shirin Qnet Ponzi.
Sanarwar ta ce, bayan kammala binciken farko da rundunar ta gudanar, an mika wadanda ake zargin bakin haure zuwa hukumar shige da fice ta kasa reshen jihar Kebbi, domin ci gaba da bincike da kuma daukar matakin da ya dace.
PR/ Abdullahi Tukur
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
