Kasuwanci
Uwargidan Gwamnan Jigawa Ta Kaddamar Da Wurin Ci Abinci Na Zamani A Maigatari
Uwargidan Gwamnan Jihar Jigawa, Hajiya Hadiza Umar Namadi ta kaddamar da wani katafaren wurin shan shayi da taliya na zamani a karamar hukumar Maigatari ta jihar.
Hajiya Hadiza Namadi ta ce, wurin sayar da shayin da taliyar da aka zamanantar da shi wani yunkuri ne na karamar hukumar ta Maigatari.

Ta kara da cewa, an tsara wannan wurin na zamani ne domin samar da yanayi mai kyau da inganci ga mutane, inda za su ci abinci cikin gamsuwa, tare da bunkasa kasuwanci a yankin.

Hajiya Hadiza ta kuma kaddamar wani tallafi ga mata 300 a karamar hukumar Maigatari.
An bayar da naira dubu talatin kowannensu, domin bunkasa kananan sana’o’i.

Gidan rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, a yayin bikin, uwargidan gwamnan, Hajiya Hadiza Umar Namadi ta gabatar da takardun kama aiki na wucin gadi ga malaman makaranta su 173.
A zantawar wakilinmu da wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, sun yabawa shugaban karamar hukumar Maigatari bisa wannan karimcin.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
