Labarai
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ya Raba Sama Da Miliyan 75 Ga Marasa Galihu
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za a ci gaba da bada tallafi ga al’umma a dukkan mazabu 30 na ‘yan majalisar dokokin Jihar.
Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi ya bada wannan tabbacin a lokacin da yake kaddamar da bada tallafi ga al’ummar karamar hukumar Miga wanda Shugaban majalisar dokokin Jihar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya raba fiye da Naira Miliyan 75 ga masu karamin karfi.

Malam Umar Namadi, ya yaba da tsarin bada tallafin ga al’ummar karamar hukumar ta Miga.
A cewarsa, tsarin bada wannan tallafi da kakakin majalisar ya yi ya dace da kudirorin gwamnatin jihar 12.

Yana mai nuni da cewar, a kowacce Karamar Hukuma za a kaddamar da irin wannan tallafi domin bunkasa tattalin arzikin al’umma don su zamo masu dogaro da kai.
Namadi, ya ce bullo da tsarin bada tallafin ya nuna cewar ‘yan majalisar Jihar suna tare da al’ummarsu.

Shi kuwa a nasa jawabin, Kakakin majalisar dokokin jihar Jigawan Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya ce rabon tallafin ya tasamma fiye da Naira Miliyan 75 wanda al’ummar mazabar Miga ne za su ci moriyar tsarin.
Ya ce tallafin zai basu damar kama sana’oi daban daban domin su zamo masu dogaro da kai.


Dangyatin, ya kuma bayyana cewar mutane kusan 2000 ne za su amfana da tallafin kudaden domin bunkasa tattalin arzikinsu.
Kakakin majalisar, ya kuma godewa Gwamna Umar Namadi bisa kyawawan kudurorinsa, gami da kulawarsa wajen ciyar da al’ummar jihar gaba.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
