Connect with us

Kasuwanci

Gwamnatin Tarayya Tare Da Hadin Gwiwar Jihar Jigawa Za Su Bunkasa Kiwon Dabbobi A Jihar

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce za ta hada gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa wajen bunkasa kiwon dabbobi domin dorewar samar da abinci da ci gaban tattalin arzikin kasar nan.

Ministan kula da ci gaban harkokin dabbobi Alhaji Idi Mukhtar Maiha ya bayyana haka, a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi a ma’aikatarsa da ke Abuja.

Ya yi nuni da cewa, wani bangare na shirin shi ne kafa jami’an hadin gwiwa don gano wuraren da za a ba da fifiko da kuma samar da manufofin da za a iya aiwatarwa cikin gaggawa.

Da yake yabawa jihar Jigawa bisa manufofinta na kiwo, ministan ya ce tsarin da gwamnatin jihar ta bullo da shi na bunkasa kiwon dabbobi abin koyi ne da ya kamata sauran jihohi su bi sahu.

Mun gudanar da kididdiga a kasa baki daya game da abubuwan da suka shafi kiwo a fadin, wadanda suka hada da wuraren kiwo, hanyoyin shanu, da ruwa da ake da shi ta hanyar madatsun ruwa, da kasuwannin kiwo a fadin kasar nan.

“Muna farin ciki da ci gaban da aka samu a jihar Jigawa.”

“Tsarin samar da zaman lafiya a jihar Jigawa a yau abin koyi ne da zan ba da shawarar sauran jihohi su koya.

“Na san jihar Jigawa ta kasance daya daga cikin yankunan da suka fi fama da matsalar manoma da makiyaya.

“Na yaba da yadda jihar take bin tsarin samar da zaman lafiya na gargajiya da muka gada a baya, a yau, babu wani makiyayi da zai shiga kowace karamar hukumar Jigawa ba tare da karbar izini ba.”Inji Ministan.

Tun da farko a jawabinsa,
Gwamna Mallam Umar Namadi, ya bayyana bangarorin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da na jihar Jigawa da suka hada da dabarun karfafa saka hannun jari a harkar kiwon dabbobi, da shata hanyoyin da dabbobi ke bi domin magance rikicin manoma da makiyaya, da sauransu.

Ya kuma jaddada mahimmancin hadin gwiwa mai karfi tsakanin gwamnatocin jihohi da ma’aikatar tarayya, domin ganin an samar da hanyoyin da ba za a iya amfana da sana’ar kiwo a Najeriya, inda ya bayyana cewa fannin na da matukar muhimmanci wajen inganta samar da abinci, da ayyukan yi, da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Mun zo nan ne domin tayaka murnar wannanmatsayi da ka samu, kun zo a daidai lokacin da aka mutukar bukatar irin wannan ma’aikatar a kasar nan.

“Wannan ma’aikatar na da matukar muhimmanci, musamman wajen tafiyar da ajandar farfado da ci gaban kasa ta  mai girma shugaban kasa, ta fuskar samar da abinci da ci gaban tattalin arzikin kasar nan

Gwamna Namadi ya ce “Mu a jihar Jigawa mun riga mun tsunduma cikin wannan fanni domin noma na cikin ajandarmu guda 12, inda aka bada fifiko  wajen bunkasa kiwon dabbobi”.

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai20 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai22 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara