Connect with us

Labarai

Mun Samar Da Kyakkyawan Tsaro Ga Masu Yi Wa Kasa Hidima-NYSC

Published

on

Darakta-Janar na Hukumar yi wa kasa hidima ta kasa NYSC, Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa masu yi wa kasa hidima a fadin kasar nan cewa ba za a tura su yankunan da ke da kalubalen tsaro ba.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga matasa masu yi wa kasa hidima da ke samun horo a sansaninsu da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Darakta Janar na NYSC wanda ke rangadi a sansanin masu yi wa kasa hidimar a jihar Zamfara, ya bayyana jin dadinsa kan yadda ak tsaurara matakan tsaro a sansanin.

Ya jaddada cewa, tsaro da jin dadin matasan na da matukar muhimmanci ga hukumar.

Birgediya Janar Ahmad ya jaddada bukatar matasan su kasance masu lura da tsaro a kodayaushe, tare da kaucewa tafiye-tafiye ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

Ya kuma ƙarfafa su da su  koyi aaƙalla sana’o’i biyu kafin su bar sansanin domin su dogara da kansu bayan sun kammala yi wa kasa hidima.

A cewarsa, hukumar NYSC za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa don tabbatar da jin dadinsu,  yana mai jaddada cewa, a kwanakin baya gwamnatin tarayya ta amince da karin alawus-alawus dinsu na wata wata.

“Gwamnatin tarayya, ta amince da karin alawus-alawus na ‘yan yi wa kasa hidima daga Naira 33,000 zuwa Naira 77,000 duk wata, muna kuma sa ran nan ba da dadewa ba za a fara aiwatar da hakan.

A nasa jawabin, Ko’odinetan NYSC a Jihar Zamfara, Malam Mohammed Lawan ya yaba wa Darakta-Janar na NYSC bisa jagorancinsa, da kuma yadda ya samar da kayan aikin da suka dace don ganin an gudanar da horaswar a jihar Zamfara cikin sauki da nasara.

Malam Lawan ya bayyana cewa, an yi wa matasa masu yi wa kasa hidima su 573 rajista a sansanin, suna kuma samun horo yadda ya dace.

Matasan sun gudanar da fareti da raye-rayen al’adu  da sauransu yayin ziyarar Darakta-Janar din.

Daga Aminu Dalhatu

Labarai

Labarai19 hours ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai1 day ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai1 day ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai1 day ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai1 day ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai2 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai2 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai3 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Labarai4 days ago

Yankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari

Daga Isma’il Adamu  An bayyana yakin neman zaben jam’iyyar APC a yankin Sanatan Funtua na Jihar Katsina a matsayin nasara,...

Labarai4 days ago

Namadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce an haɗa kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa...

Mafi Shahara