Labarai
Saura Kiris Mu Kai Ga Bello Turji – Rundunar Sojan Nijeriya
Kwamandan runduna ta 1 ta sojojin Najeriya Gusau, Birgediya Janar Opurum Timothy, ya baiwa al’ummar jihar Zamfara aniyar rundunar sojojin Najeriya wajen ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron rundunar sojojin Najeriya ta yammacin Afirka WASA 2024 da aka gudanar a Gusau.
Kungiyar WASA wani taron ne na shekara-shekara da rundunar sojojin Najeriya ke shiryawa domin murnar dimbin al’adun gargajiya na wannan kasa mai girma.
Taron na shekara-shekara yana tattaro Jami’ai, Sojoji, da iyalansu a cikin annashuwa don bikin da kuma nuna ƙarshen ayyukan shekara.
Janar Opurum wanda ya jaddada kudirin rundunar na kawar da ‘yan fashi daji da kuma dawo da zaman lafiya a Zamfara da yankin Arewa maso Yamma gaba daya, ya yi kira ga sojojin da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu, yana mai jaddada cewa, sadaukarwarsu na da matukar muhimmanci wajen samun zaman lafiya mai dorewa.
A cewarsa, a halin yanzu fitaccen jagoran ‘yan bindigar Bello Turji na kan hanyarsa ta zuwa lahira saboda hare-haren da sojoji ke kai wa a jihar Zamfara.
“Bello Turji matsoraci ne kuma ya yi watsi dadakarunsa saboda matsin lamba da muka yi masa. Mun share da yawa daga cikinsu kuma za mu ci gaba da ci gaba da kai farmakin kai tsaye zuwa maboyarsu.”
Kwamandan Birgediya wanda ake yi wa lakabi da “Jar Kunama”, ya yabawa al’ummar Zamfara bisa yadda suke ba da hadin kai, musamman ta hanyar samar da muhimman bayanan sirri, wanda ya haifar da gagarumar nasara.
Tun da farko, Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara, wanda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Meriga ya wakilta, ya yabawa rundunar sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro bisa namijin kokarin da suke yi na samar da zaman lafiya mai dorewa a fadin jihar ta Zamfara.
Taron WASA na bana a Gusau ya samu halartar manyan baki da suka hada da sarakunan gargajiya da shugabannin sauran hukumomin tsaro kamar rundunar sojojin saman Najeriya da jami’an tsaro da dai sauransu.
Muhimman abubuwan da suka faru a wajen taron sun hada da yawon shakatawa, baje kolin al’adu da raye-raye, wasan taekwondo, tuggun yaki, da kunna wuta da Kwamandan Brigade ya yi da dai sauransu.
Yayin da wasu da dama da suka yi nasara suka je gida da kyaututtuka daban-daban.
COV/AMINU DALHATU/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
