Labarai
RSF da rundunar sojin Sudan sun kashe mutum 190 a Darfur
Ƙungiyar likitocin Sudan ta zargi sojojin ƙasar da dakarun RSF da kashe kusan mutum 200 a gumurzun da suke yi a wasu yankuna da ke yankin Dafur, kamar yadda jaridar intanet ta Sudan Tribute ta ruwaito.
“Rahoton ƙungiyar ya gano an kashe mutum 190, sannan an jikkata wasu guda 106 a sanadiyar ruwan bama-bamai a tsakanin ɓangarorin biyu a kudanci da arewacin Dafur a ƴan kwanakin nan.”
Rahoton ya nuna cewa dakarun RSF sun kashe sama da mutum 30, ciki har da mata da ƙananan yara a al-Fashir, sannan sojoji sun kashe mutum 115 a Kabkabiya da wasu mutum 45 a Nyala a kudancin Dafur.
A ƴan makonnin da ake ciki, sojojin Sudan sun ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare a kan dakarun RSF a Dafur.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
