Ilimi
Sabbin kwamishinonin Jihar Kano Bakwai da Ma’aikatunsu
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci rantsar da sabbin kwamishinoni bakwai da ya nada.
Kwamishinan shari’a na Kano Kuma babban lauyan jihar, Barista Haruna Isa Dederi ne ya rantsar da sabbin kwamishinonin tare da sauran masu ba Gwamna shawara.
Har ila yau dai Gwamnan ya jagoranci rantsar da sabbin manyan sakatarori Shida da aka daga likkafar su zuwa mataki a aikin Gwamnati da kuma rantsar da masu bashi shawara 13 daga cikin 15 da aka nada
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya tura sabbin kwamishinonin zuwa ma’aikatun da aka tanadar musu.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da tura su ma’aikatun da zasu jagoranta kamar haka.
Alhaji Shehu Wada Sagagi zai kula da ma’aikatar kasuwanci da zuba jari ta kano. Kwamared Ibrahim Abdullahi Waya, ma’aikatar kula da yada Labarai ta Kano. Sai Dakta Dahir Muhammad Hashim an amince ya rike ma’aikatar kula da Muhalli ta kano
Sauran su ne Abdulkadir Abdussalam, ma’aikatar kula da Raya karkara ta Kano. Dakta. Isma’ila Aliyu Dan Maraya, ma’aikatar kula da Kudi ta Kano. Dakta Gaddafi Sani Yakubu kuwa ma’aikatar Kula da makamashi ta Kano
Sai kuma Dakta.Nura Iro Ma’aji , ma’aikatar Kula da bada kwangiloli da bibiyar ayyukan gwamnati
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce ya dauki matakin samar da sabbin kwamishinonin ne domin inganta ayyukan gwamnati da Kuma kawo ci gaba a Kano.
Abdullahi Jalaluddeen, Kano/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
