Labarai
Hukumar Fansho Ta Jihar Jigawa Ta Biya Naira Biliyan 1.5 Ga ‘Yan Fansho 609
Hukumar Fansho ta Jihar Jigawa ta biya sama da Naira Biliyan daya da rabi ga mutane 609 da suka yi ritaya daga aiki bayan sun kai shekaru 35 suna aiki, a tsakanin watannin Agusta zuwa Disamban bara.
Shugaban hukumar Dakta Bilyaminu Shitu Aminu ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga wadanda suka ci gajiyar tallafin aa ofishin ffansho da ke Dutse.
A cewarsa, biyan kudin ya kasu kashi hudu ne, wanda ya nuna cewa kashi na farko na ma’aikata 465 da suka yi ritaya sun kunshi wadanda ko dai sun kai shekaru 35 suna aiki, ko kuma shekara sittin na haihuwa, inda aka biya sama da Naira Biliyan daya miliyan dari 1 da saba’inda uku.
Ya ce, kashi na biyu na ma’aikata 103 su ne wadanda suka mutu a lokacin da suke bakin aiki, inda aka biya magadansu sama da Naira miliyan 315.
Dokta Bilyaminu Shitu ya ci gaba da bayyana cewa, kashi na uku ya kunshi ma’aikata 39 da suka yi ritaya daga aiki kuma suka fara karbar fansho duk wata amma sun mutu kafin su kai wa’adin mafi karancin shekaru biyar bayan ritayar, da aka biya sama da Naira miliyan 54.
“Kashi na karshe shi ne wanda ya ci gajiyar tallafin wanda bai kai shekara 5 ba, kuma doka ta bayyana cewa duk ma’aikacin da ya cancanci a biya shi daga tsarin shi ne ya ba da gudummawar na tsawon shekaru biyar. A karkashin wannan fanni, mun biya mutum biyu, kinanin Naira 750, ciki har da kashi 15 bisa dari a matsayin riba“.
Shugaban hukumar ya gargadi ‘yan fansho a fadin jihar da su yi hattara da masu damfara.
Ya kara da cewa, ayyukansu kyauta ne, a don haka ya bukaci masu karbar fansho da jada su ba wani ma’aikaci cin hanci kafin su karbi hakkinsu.
Bilyaminu Shitu ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar da su ci gaba da marawa Gwamnati baya da addu’o’insu, domin ganin an samu Jihar Jigawa mai inganci da kowa zai samu kwanciyar hankali a cikin ajandar ci gaban Jihar.
Ya kuma yabawa Gwamna Umar Namadi bisa kulawar da yake baiwa ‘yan fansho a jihar.
“Biyan fansho da giratuti da aka yi cikin gaggawa ya taimaka wajen kawar da matsin rayuwa ga ’yan fansho”. Inji shi.
Ya bayyana cewa wannan karimcin zai inganta rayuwa tare da karfafa jin dadin wadanda suka yi ritaya.
“Gwamnatin jihar da hukumar za ta ci gaba da tabbatar da biyan fansho cikin gaggawa da sauran hakkokin ma’aikata domin samar da ingantacciyar hidima, jin dadin wadanda suka yi ritaya .”
Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar kudaden fanshon, sun yabawa Gwamnan kan yadda ya ba da fifiko kan al’amuran da suka shafi jin dadin ‘yan Fansho.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
